
An samu mai cutar Corona a Adamawa a karon farko
Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da samun mutum na farko da ke dauke da cutar korona.
Gwmanan jihar, Ahmadu Fintiri ya sanar da hakan ne a wani jawabi da ya yi ta kafar sada zumunta na Facebook, inda ya ce jihar za ta dauki tsauraran matakai wajen dakile bazuwar cutar annobar a jihar.
Daga cikin matakan da gwamnan ya lissafa akwai rufe iyakokin jihar domin gudun kwararar makwabta zuwa cikin Adamawar, inda ya nemi hadin kan jami'an tsaro da su sanya ido.