
Shugaba Buhari ya aikewa jama’ar Adamawa sakon ta’aziyya kan harin Boko Haram
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aikewa jama'ar garin Kwapree na jihar Adamawa sakon ta'aziyya kan harin da Boko Haram ta kai musu.
Sakon na shugaban kasar ya isa ne ta bakin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha inda yace Shugaba Buhati na mikawa jama'ar garin dake karamar Hukumar Hong sakon jaje.
Yace gwamnati zata dauki matakin magance matsalar da kuma taimakawa jama'ar garin sake gina garin nasu.
Yace ya shaida cewa an lalata sama da 78 da kuma Shaguna 12