fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Adams Oshiomhole

Ba ni da sha’awar dawowa a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa>>Oshiomhole

Ba ni da sha’awar dawowa a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa>>Oshiomhole

Siyasa
Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC mai mulki, Kwamared Adams Oshiomhole ya nesanta kansa daga jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirya makarkashiyar komawa ofis sakamakon karar da wata kotu ta shigar game da jagorancin Mai Mala Buni karkashin jagorancin Mai Kula da Babban Taron Kasa. A cikin wata sanarwa a daren Litinin, Oshiomhole ya ce matsayinsa bai canza ba kuma ko da Kwamitin Gudanarwar Kasa na NEC na jam’iyyar sun gayyace shi ya koma kujerarsa, zai yi watsi da wannan tayi
Bangaren Oshiomhole sun maka jam’iyyar APC a Kotu

Bangaren Oshiomhole sun maka jam’iyyar APC a Kotu

Siyasa
Bangaren Kwamitin Zartaswa na jam'iyyar APC, na tsohon shugaban jam'iyyar,  Adams Oshiomhole ya maka jam'iyyar APC a kotu.   Hillary Eta wanda shine tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin Kudu maso Kudu ne ya kai karar ranar 26 ga watan Nuwamba.   Yana neman a dakatar da kwamitin rikon kwarya na Gwamna Mai Mala Buni daga gudanar da duk wani aiki na jam'iyyar. Yace doka bata baiwa Gwamna Buni dama ya rike mukamin rikon kwaryar ba a matsayinsa na Gwamna.   Hakanan Doka bata bayar da damar a yiwa zababbun shuwagabannin jam'iyyar abinda aka musu ba. Dan hakane yake neman kotun ta rusa wancan kwamiti na Buni kada ya ci gaba da gudanar da jam'Iyyar. The plaintiffs argued among others that by virtue of Section 183 of the Nigerian Constitution and Ar...
Sakamakon Zaben Edo: Saida na zubar da hawaye, Adams Oshiomhole

Sakamakon Zaben Edo: Saida na zubar da hawaye, Adams Oshiomhole

Siyasa
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa sai da ya zubar da hawaye saboda zaben na jiharsa wanda abokin hamayyarsa, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe.   Oshiomhole ya bayyana hakane a wani faifan Bidiyo daya bayyana daya bayyana wanda shine karon farko da yayi magana tun bayan fitar sakamakon zaben. Yace a rayuwa dama mutum yana iya yinsa ne ya barwa Allah sauran, yace da yaga yanda tsaffi ke fitowa, basu gajiya ba suna zabe sai da ya zubar da kwalla.   Yace kuma hakan ya bashi karfin gwiwar mantawa da abinda ya faru a baya dan ci gaba da fafutuka.   Oshiomhole ya jawo hankalin 'yan Najeriya da a ci gaba da ganin ana karfafa Dimokradiyyar kasarnan domin itace dai kasar mu wadda bamu da kamarta.
Duk da shugaba Buhari da APC sun amince da zaben Edo da taya Obaseki Murna, Tinubu da Oshiomhole sun yi Gum

Duk da shugaba Buhari da APC sun amince da zaben Edo da taya Obaseki Murna, Tinubu da Oshiomhole sun yi Gum

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo wanda dan takarar PDP, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe inda ma har ya taya gwamnan murnar lashe zaben.   Hakanam uwar jam'iyyar APC ta kasa ta bakin shugaban ta na Riko, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ta amince da sakamakon inda itama ta taya Gwamna Obaseki murna. Saidai duk da haka Adams Oshiomhole da Bola Ahmad Tinubu wanda duka sun yi kamfe din kada a zabi Obaseki har yanzu basu ce komai ba.   Rigima da Oshiomhole da Tinubu ta kai ga Oshiomholen ya rasa kujerarsa ta shugaban jam'iyyar APC sannan kuma Obaseki ya bar APC bayan da aka hanashi takarar gwamna a jam'iyyar inda ya koma PDP.   A maganar da yayi da manema labarai, Obaseki ya bayyana Oshiomhole da Tinubu a mat...
Ba mutunci zan yi maganin Oshiomhole>>Obaseki

Ba mutunci zan yi maganin Oshiomhole>>Obaseki

Siyasa
Gwamnan jihar Edo,  Godwin Obaseki yayi magana bayan lashe zaben da yayi a karo na biyu inda yace muddin tsohon uban gidansa, Adams Oshiomhole bai canja abinda yake ba to zai dandana kudarsa.   Obaseki ya bayyana hakane a ganawa ta musamman da yayi da gidan talabijin din Arise inda aka tambayeshi ka  rade-radin dake yawo cewa wai zai kori Oshiomhole daga jihar. Yace wannan ba gaskiya bane amma idan Oshiomholen be kama girmansa ba ya ci gaba da daukar nauyin wasu suna abinda bashi kenan ba to zai dandana kudarsa dan zai rufe ido yayi maganinsa.   Da yake Magana akan Tinubu da irin rawar da ya taka a kan maganar sake zaben sa, yace Tinubu da Oshiomhole suna da wata halayya wadda suke so su rikawa mutane karfa-karfa amma maganar gaskiya itace idan basu canja ba do...
Yawancin tsaffin gwamnonin PDP basa iya fitowa cikin jama’a ba tare da an bisu da Jifa ba>>Adams Oshiomhole

Yawancin tsaffin gwamnonin PDP basa iya fitowa cikin jama’a ba tare da an bisu da Jifa ba>>Adams Oshiomhole

Uncategorized
Tsohon gwamnan jihar Edo wanda kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC ne, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa, yawancin tsaffin gwamnonin PDP basa iya shiga cikin jama'a saboda tsoron jifa.   Ya bayyana hakane a yayin da aka yi gawa dashi a gidan talabijin na Channelstv inda yake bugun kirji kan yanda yake da samun karbuwa a wajen jama'ar jiharsa. Yace shin kaga yanda mutane suka tarbeni a wajan yakin neman zabe? Yace amma da yawan tsaffin gwamnonin PDP bama a jihar kadai ba ba zasu iya shiga cikin jama'a ba saboda tsoron jifa.
Kasheni aka so ayi>>Adams Oshiomhole ya fada kan hadarin da tawagar motocin sa suka yi

Kasheni aka so ayi>>Adams Oshiomhole ya fada kan hadarin da tawagar motocin sa suka yi

Siyasa
A jiyane Rahotanni suka bayyana cewa tawagar tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole ta yi hadari inda har 'yansanda 2 suka rasu wasu kuma suka jikkata.   Da yake magana ta bakin kakakinsa, Victor Oshioke ,Adams Oshiomhole ya bayyana cewa kasheshi aka so yi. Yace wanda suka ga yanda lamarin ya faru sun gaya musu cewa kashesu aka so yi kuma suma sun yadda da hakan domin ba gudu suke ba yayin da lamarun ya faru.
Yan Sanda 2 Sun Rasu, Oshiomhole ya tsallake Rijiya da baya a hadarin daya Afkawa tawagarsa

Yan Sanda 2 Sun Rasu, Oshiomhole ya tsallake Rijiya da baya a hadarin daya Afkawa tawagarsa

Uncategorized
Yan sanda biyu sun rasa rayukansu a wani hadari da ya hada da ayarin motocin Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a ranar Talata. Oshiomhole da tawagar yakin neman zaben APC na kan hanyarsu ta zuwa Usen a karamar hukumar Ovia kudu maso gabas ta jihar Edo lokacin da hatsarin ya faru. Da yake magana a kan lamarin, dan takarar gwamna na APC, Osagie Ize-Iyamu, ya ce za a iya fassara hatsarin a matsayin yunkurin kashe Oshiomhole. Ya kuma sanar da dakatarwa na awanni 24 na kamfen dinsa don girmama jami'an da suka mutu.
Bidiyo: Kalli yanda Oshiomhole da shugaban fadar shugaba Buhari ke kuskus din a kama wasu a fadar shugaban kasar

Bidiyo: Kalli yanda Oshiomhole da shugaban fadar shugaba Buhari ke kuskus din a kama wasu a fadar shugaban kasar

Siyasa
A jiyane dai cece-kuce ya barke tsakanin 'yan Najeriya bayan bayyanawar wani bidiyo na sirri da aka dauka a boye a fadar shugaban kasa.   Bidiyon ya nuna yanda tsohon shugban jam'iyyar APC,  Adams Oshiomhole da Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa,  Ibrahim Gambari suke tattauna kamen da zaa wa wasu. PDP ta yi zargin cewa Membobin jam'iyyar Adawane za'a kama saidai fadar shugaban kasa tace masu tada zaune tsaye ne suka fitar da Bidiyon.