A yau, Litinin ne tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya je fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda suka gana.
Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani akan tattaunawar tasu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yanzu haka yana ganawa da tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Adams Oshiomhole, a fadar shugaban kasa, Abuja.
SaharaReporters sun tattaro cewa Oshiomhole, ya isa Villa da misalin karfe 2:50 na rana.
Kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar APC a ranar 25 ga watan Yuni ya wargaza Kwamitin Gudanar da Jam’iyyar na kasa wanda Oshomhole ya jagoranta.
Wannan bidiyon ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda ake dangantashi da zaben jihar Edo.
Anga tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole na rawa wanda rahotanni suka bayyana cewa wajan yakin neman zabene.
https://www.youtube.com/watch?v=GPwgMsedir8
Oshiomhole dai dama a lokuta da yawa a baya yakan yi rawa a wajan yakin neman zabe.
Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya bayyana cewa jam'iyyar APC zata watse ta yanda ba zata taba dawowa daidai ba.
Buba ya bayyana hakane a sabuwar tattaunawar da yayi da manema labaran Vanguard inda yace a yanzu haka jam'iyyar ta rabu zuwa kashi-kashi.
Yace tun a baya yayi gargadin cewa Adams Oshiomhole da aka nada a jam'iyyar(dan ba zabenshi aka yi ba) zai wargazara ne. Yace wanda suka sashi ya musu aiki saboda sun san mutum ne me rawar kai shiyasa suka sashi, yace gashi kuma ta faru.
Yace a yanzu akwai bangaren shugaban kasa, da bangaren Tinubu, dana El-Rufai, gwamnan Kaduna da kuma na gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu. Yace Oshiomhole ba zai tana iya kai APC ko shugaban kasa kotu ba saboda suna da abinda zasu kamashi dashi,...
Kotun daukaka kara dake zamanta a babban birnin tarayya, Abuja ta kori karar da tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya shigar inda yake kalubalantar dakatar dashi da aka yi.
Da yake gabatar da hukuncin watsi da karar, Mai shari'a, Uchechukwu Onyemenam da ya jagoranci alkalai 3 a jiya, Talata, 30 ga watan Yuni ya bayyana korafin na Oshiomhole a matsayin marar shaidar da za'a iya amsa.
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC a shirye take ta kori tsohon shugaban ta, Adams Oshiomhole daga cikinta kwata-kwata bayan da ya rasa mukaminshi na shugaban jam'iyyar.
Kwamitin gudanarwar jam'iyyar da yayi taronshi na farko karkashin shugaban jam'iyyar na riko, Victor Giadom a fadar shugaban kasa, bisa jagorancin shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya rushe kwamitin gudanarwa na Adams Oshiomhole me membobi 18.
Wannan dalili ne yasa bangaren dake goyo bayan Oshiomhole yayi barazanar zuwa kotu saboda wannan mataki.
Rahotanni dai sun bayyana cewa shugaba Buharine ya bada shawarar rushe kwamitin na Adams Oshiomhole, kamar yanda hadimin shugaban, Bashir Ahmad ya bayyana.
Wata majiya a jam'iyyar ta bayyanawa Punch cewa wannan mataki da bangare...
A jiyane dai ta bayyana a fili cewa APC ta rufe shafin tsohon shugaban ta, Adams Oshiomhole bayan da aka yi taron koli na jam'iyyar a fadar shugaban kasa dake tabbatar da Victor Giadom a matsayin shugaban riko na jam'iyyar.
Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu akan wannan lamari. Daya daga cikin wanda suka bayyana ra'ayoyinsu shine Sanata Dino Melaye.
Yayi Bidiyo inda yake wa Adams Oshiomhole kwalo da habaicin(Allah kara).
Kalli bidiyon a kasa:
https://twitter.com/dino_melaye/status/1276207884632801283?s=19
Dino Melaye da na daga cikin wanda ke bayyana ra'ayoyinsu akan abubuwa da dama dake faruwa a kasarnan daga lokaci zuwa lokaci.
An nada gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC.
Kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar ne ya dauki wannan mataki bayan da ya soke kwamitin rikon APC din a wani taro da ya gudanar a ranar Alhamis da rana.
Hakan ya biyo bayan shawarwarin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar ne, kamar yadda mai taimaka masa kan shufakan sada zumunta Bashir Ahmed ya fada a shafinsa na Twitter.
Jam'iyyar APC dai na ta fuskantar matsaloli a baya-bayan da suka shafi shugabancinta.
Jam'iyyar All Progressives Congress APC, ta wargaza Kwamitin Gudanar ta Kasa.
An yanke hukuncin ne a taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar ranar alhamis.
Bashir Ahmad, mataimaki ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana a shafin sa na Twitter cewa, "Bayan shawarar Shugaba Muhammadu Buhari, Kwamitin Kasa (NWC) na Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta rushe."
Mukaddashin shugaban APC, Victor Giadom ya nada gwamnan Yobe, Mai-Mala Buni a matsayin sabon shugaban kwamitin wucin gadi kuma nan take ministan shari'a, Abubakar Malami ya rantsar dashi.
Wannan mataki na nuni da cewa an gama da zancen Adams Oshiomhole.
Kwamitin zartarwa na karamar hukuma 10 a Etsako ta yamma ta All Progressives Congress (APC) a jihar Edo ta janye dakatarwar da akema Adams Oshiomhole a matsayin memba na jam’iyyar.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, Emuakemeh Sule, sakataren sashen, mambobi 17 daga 26 sun sanya hannu kan kudurin.
Jam’iyyar ta dakatar da Oshiomhole ne a watan Nuwamba sakamakon takaddama mai yawa da ya yi da Godwin Obaseki, gwamnan Edo.
A bisa wannan dalilin ne wata babbar kotu a yankin babban birnin tarayya (FCT) ta ba da umarnin dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.