
Oshiomhole ya amince da umarnin kotu
Dakataccen Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa ya karbi kaddarar hukumcin Babbar Kotun Daukaka Kara ta Tarayya, wadda ta jaddada dakatarwar da Babbar Kotun Abuja ta yi masa.
Da ake tattaunawa da shi, Oshiomhole ya ce amince da hukuncin kotu, kuma tuni ya janye daga kan kujerar shugabancin Jam’iyyar APC, har an nada na riko.
Ya ce shi mutum ne mai bin umarnin kotu. Don haka ya rungumi kaddara, amma kuma zai tuntubi lauyoyin sa, domin su ba shi shawarar mataki na gaba da zai dauka.
Mataki daya tal ne dai ya rage wa Oshiomhole, shi ne na garzayawa Kotun Koli.
Kotu ta jaddada dakatar da shi a daidai lokacin da APC ke cikin ruguguwar rudanin zaben gwamnan jihar Edo, jihar da Oshiomhole ya fito, inda kuma ya yi gwamna tsawon shekaru takwas.
...