fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: Adams Oshionhole

Kotu ta yi watsi da bukatar Oshiomhole na a mayar dashi shugaban APC

Kotu ta yi watsi da bukatar Oshiomhole na a mayar dashi shugaban APC

Siyasa
Kotun daukaka kara dake zamanta a babban birnin tarayya, Abuja ta kori karar da tsohon shugaban jam'iyyar APC,  Adams Oshiomhole ya shigar inda yake kalubalantar dakatar dashi da aka yi. Da yake gabatar da hukuncin watsi da karar, Mai shari'a, Uchechukwu Onyemenam da ya jagoranci alkalai 3 a jiya, Talata, 30 ga watan Yuni ya bayyana korafin na Oshiomhole a matsayin marar shaidar da za'a iya amsa.
Ina Alfahari da Nasarar da muka samu a jihar Kwara>>Adams Oshiomhole

Ina Alfahari da Nasarar da muka samu a jihar Kwara>>Adams Oshiomhole

Uncategorized
Tsohin shugaban APC, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa babbar nasarar da ya samu kuma yake Alfahari da ita a matsayin shi na shugaban APC, itace nasarar da suka samu a jihar Kwara.   Yace bai damu da abinda mutane zasu ce ba amma shi nasarar jihar Kwara ta fiye mai kowace. Ya kara da cewa kwato jihar Gombe daga hannun PDP ma na daya daga cikin abinda ba zai manta ba. Saidai yace babu wani abu da yayi a matsayinshi da shugaban APC da yake nadama.   Ya kuma bayyana cewa ya amince da rushe kwamitin gudanarwar da jam'iyyar ta yi.
APC ba jam’iyyar kama karya bace ko Shugaba Buhari yana bin dokokin jam’iyya>>Adams Oshiomhole yayi magana kan hana gwamna Obaseki takara

APC ba jam’iyyar kama karya bace ko Shugaba Buhari yana bin dokokin jam’iyya>>Adams Oshiomhole yayi magana kan hana gwamna Obaseki takara

Siyasa
Shugaban jam'iyyar APC,Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam'iyyarsu ba ta kama karya bace dan ko shugaban kasa,Muhammadu Buhati na bun dokokinta.   Oshiomhole ya bayyana hakane bayan ganawar da kwamitin jam'iyyar yayi da shugaban ma'aikatan shugaban kasa,  Farfesa Gambari a jiya.   Da yake amsa tambaya kan hana gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki takara a jam'iyyar, Oshiomhole yace idan za'a iya tunawa a lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke neman sake tsayawa takara a karo na 2 saida aka yi zaben fidda gwani dan haka babu wanda zasu dagawa kafa dan jam'iyyarsu bata manyan mutane bace.
Na yi nadamar abubuwan da na yi>>Shugaban APC

Na yi nadamar abubuwan da na yi>>Shugaban APC

Siyasa
Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Adams Oshiomhole ya ce, ya gane kuskurensa dangane da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ya kuma kusa raba shi da mukaminsa, kuma yanzu haka a shirye yake ya yi aiki da sauran shugabannin jam’iyyar a cewarsa.   Yayin da yake jawabi bayan ya koma ofishinsa sakamakon umurnin kotun daukaka kara na jingine hukuncin wata kotun tarayya, Oshiomhole ya ce an tilasta masa ya amince da cewa, ba shi ne shugaban da ya fi kowa kwarewa ba, amma kuma babu wanda bai amince da jajircewarsa ba.   Shugaban ya ce, ya fahimci muhimmancin sasantawa da jama’a kan yadda yake gudanar da mulkinsa domin ganin an fahimci juna wajen yin aki tare.   An dai samu rarrabuwar kawuna ne tsakanin masu goyan bayan shugaban da masu adawa da shi sakamak...
Kotu ta bada umarnin Oshiomhole ya koma mukaminsa

Kotu ta bada umarnin Oshiomhole ya koma mukaminsa

Siyasa
Wata babbar kotun tarayya a Kano ta jingine hukuncin da babbar kotu a Abuja ta yanke na dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole daga mukaminsa.   Mai shari’a Lewis Allagoa, ne ya sanar da yanke wannan hukuncin yau Alhamis, sannan ya umarci rundunar ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya DSS su bai wa Oshiomhole tsaro domin ya koma ofishinsa.