fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Adamu Adamu

Yajin aikin da ASUU ke yi yanzu laifin gwamnatin data gabata ne>>Minista Adamu Adamu

Yajin aikin da ASUU ke yi yanzu laifin gwamnatin data gabata ne>>Minista Adamu Adamu

Siyasa
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya dorawa gwamnatin data gabata laifin yajin aikin da malaman jami'a ke yi karkashin kungiyareu ta ASUU.   Yajin aikin da a yanzu ya kai wajan watanni 8 kenan malam jami'ar sun bayyana cewa suna yinda ne saboda gwamnati ta ki amincewa ta ciresu daga tsarin IPPIS. Minista Adamu Adamu ya bayyana hakane jiya a Abuja inda yace ko kadan gwamnatin data gabata bata kyauta musu ba dan ita ta jawo wannan matsalar da ake ciki. Yace gwamnatin ta amince ta baiwa malaman jami'ar Tiriliyan 1.3 wanda kuma tasan abune ba mai yiyuwa ba.   Yace amma dai suna nan suna tattaunawa da malaman jami'ar kuma nan bada jimawa ba suna tsammanin za'a samu mafita.   “I do believe that while they were signing that agreement, they knew that it is not pos...
Ministan Ilimi ya nemi wadanda su kai garkuwa da Daluban da a ka sace da su gaggauta sakin su

Ministan Ilimi ya nemi wadanda su kai garkuwa da Daluban da a ka sace da su gaggauta sakin su

Tsaro
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya nuna bacin ran sa game da hare-hare da ake kaiwa cibiyoyin ilimi a kasar nan. Ministan yayi wannan furucin ne a ranar Laraba, 9 ga Satumbar, 2020 yayin bikin ranar kare ilimi daga hare-hare na Duniya, Inda yayi tir da hare-haren da ake kaiwa makarantu tare da danganta hakan a matsayin take hakkin dalibai na samun ingantaccen ilimi. Malam Adamu ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya tana iya kokarin ta wajan kare cibiyoyin koyo daga kowane irin hari. Ya kuma yi kira da masu garkuwa da mutane da su kai awon gaba da wasu Dalibai a jihar kaduna da su gaggauta sakin su. A karshe ya bukaci hukumomin tsaro da su kara dage dantsi wajan kare makarantu a fadin kasar.
Iyayen Dalibai zasu zauna da Gwamnatin tarayya dan neman a bar ‘ya’yansu su rubuta WAEC

Iyayen Dalibai zasu zauna da Gwamnatin tarayya dan neman a bar ‘ya’yansu su rubuta WAEC

Uncategorized
Kungiyar Iyay dalibai na Najeriya, NAPTAN ta bayyana cewa bata ji dadin yanda gwamnatin tarayya ta yanke shawarar cewa ba zata bar 'ya'yansu rubuta jarabawar WAEC da NECO na wannan shekarar ba.   Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Haruna Danjima ne ya bayyanawa manema labarai haka inda yace zasu zauna da gwamnatin dan jin yanda za'ayi a samu a bude musu makarantu. Ya kara da cewa a baya sun shirya zasu hada hannu da makarantu dan samar da abin wanke hannu da sauran abubuwan kariya daga cutar Coronavirus amma kwatsam sai suka ji wannan sanarwa.