fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Tag: Addini

Kalli wani dan kasar China daya musulunta har ya samu matar aure

Uncategorized
Allah buwayi gagara misali, me shirya wanda yaso a lokacin da yaso, wani jar fatane dan kasar China Rahotanni suka tabbatar cewa ya amshi addinin Musulunci a Jihar Filato inda ya zabi sunan Samir kuma har ya samu matar aure. Lamarin ya farune a karamar hukumar Wase dake jihar, kamar yanda jaridar Rariya ta ruwaito. Muna fatan Allah ya karamai Imani da soyayyar addini ya kuma karo mana irinshi.

An yi ‘yar tsana me hijabi ta farko a Duniya dan karrama ba’amurkiya me kishin addinin islama

Uncategorized
Wani kamfanin yin 'yar tsana me suna Barbie, yayi 'yar tsana me hijabi ta farko a Duniya dan karrama ba'a murkiyarnan me kishin addinin musulunci wadda duk inda zata shiga, sanye take da hijabi, watau Ibtihaj Muhammad. Ita dai Ibtihaj Muhammad 'yar kasar Amurkace kuma musulma, tana wasan wuka a gasar Olympic, kuma tayi suna a matsayin mace ba'amurkiya, musulma ta farko data taba zuwa gurin wasannin Olympic sanye da hijabi.

Nasiha daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Uncategorized
zamo na kowa koda kowa bai zamo naka ba. Yiwa kowa fatan alheri koda akwai masu yima fatan sharri, saka dukkanin musulmi a cikin addu'arka koda babu mai sakaka a cikin addu'arsa. Nufi kowa da alheri koda akwai masu nufanka da sharri. Kyautata tsakaninka da Allah kada kadamu da abinda mutane suke cewa akanka. Allah ya kyautata rayuwarmu Ameen.

Wani mutum ya hana diyarshi amsa tambayar da akayi mata daga makaranta a kasar Ingila na cewa ta rubutawa iyayenta wasika zata shiga addinin musulunci

Uncategorized
Wani uba a kasar Ingila ya hana diyarshi yin aikin gida da aka bata daga makaranta saboda an tambayeta ta rubutawa iyayenta wasika akan tana son karbar addinin musulunci, kamar yanda ake ganin hotonnan na sama yana dauke da tambayar da aka yiwa yarinyar 'yar shekari 12 akace taje gida ta amsa. Koda akayi arashi mahaifinta ya ga wannan tambaya da aka yi mata sai ya hanata amsa tambayar Sannan kuma ya tafi makarantar dan yaji ba'asi akan dalilin da yasa za'a sa 'yarshi ta rubuta musu cewa zata canja addini, mutumin me suna Mark ya bayyana cewa baya inkarin cewa a fahimtar da yara addinai daban-daban tunda yasan cewa hakan yana cikin tsarin koyarwa na kasar. Amma abinda ya daure mishi kai shine yanda za'a tambayi yarinya 'yar shekaru 12 ta rubutawa iyayenta cewa zata canja addi...

Yanda wani me horar da sojoji a kasar Amurka ke saka sojoji musulmai cikin injin wanki yana kunnashi dan ya azabtar dasu kawai dan suna musulmai

Uncategorized
An kama wani tsohon sojan kasar Amurka aka kuma gabatar dashi gaban kuliya, manta sabo dan yimai hukunci akan irin azabtarwar da yake yiwa sabbin sojoji musulmai da ake horar dasu dan zama gwanaye, shidai wannan soja dan shekaru 34 shaidun gani da ido sun tabbar da cewa yana ware sojoji musulmai lokacin da yake bayar da horaswa sannan ya rika kiransu da sunan 'yan ta'adda, 'yan kungiyar ISIS. Sannan kuma ya umarcesu shiga wani injin wanki ya kuma kunna injin wankin dan azabtarwa kawai dan suna musulmai. Saidai lauyan sojan da ake kara ya ya musanta wannan zargi inda yace tsohon sojan besan cewa sojojin da yake horaswa musulmai bane, kuma yana basu horaswa irin wadda ake baiwa kowane soja. Amma kotu tayi bincike kuma ta tabbatar da wannan laifi na wannan soja me suna Felix sannan ta t...

Wani Inyamuri daga jihar Imo ya musulunta: Ya zabi sunan ‘Yusuf’

Uncategorized
Wannan wani Inyamurine daga jihar Imo da Allah ya azurtashi da hasken zuciya ya amshi kalmar shahada jiya Juma'a kamar yanda wani wanda shima musulmin inyamurinne ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta da muhawara, shi dai wannan bawan Allah ya zabi sunan Yusuf bayan da ya yi kalmar shada. Muna mai fatan Allah ya kara fahimtar dashi addinin musulunci kuma ya karo mana irinsu. ko da a satin daya gabata an samu wata baiwar Allah me suna A'ishat Obi daga dai jihar ta Imo inda ta fito tace ina alfahari da kasancewata musulma , kuma ta karfafawa 'yan uwanta inyamurai gwiwa akan su fito su daina jin tsoron karbar addinin musulunci, kuma su tashi su nemi ilimin addinin.

Shugaba Buhari ya gana da malaman addini a fadarshi

Uncategorized
A yau Juma'ane shugaban kasa Muhammadu Buhari ga mataimakinshi farfesa Yemi Osinbajo tare da wasu ministoci suka gana da shuwagabanin addinan Musulunci dana kirista a fadar shugaban kasar, a lokacin ziyarar tasu shugaba Buhari yayi alkawarin gyara sukar da akewa gwamnatinshi na cewa ta bayar da mukamai ga 'yan Arewa fiye da 'yan kudu. Ya kara da cewa ya bayar da umarnin a kawomai sunayen shuwagabannin ma'aikatan dake rike da manyan ma'aikatun gwamnatin nashi dan ya duba yayi gayaran daya kamata. Haka shugaba Buhari yayi alkawarin ganin ya kula da bangaren shari'a da kuma jami'an tsaro dan ganin an samu zaman lafiya me dorewa a kasarnan.