fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Ado gwamja

Hisbah ta kama karamin Yaro masoyin Ado Gwanja

Hisbah ta kama karamin Yaro masoyin Ado Gwanja

Nishaɗi
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani kankanin yaro mai suna Abdullahi Muhammad dan asalin karamar hukumar Shelang ta jihar Adamawa, wanda ya zo Kano domin haduwa da fitaccen mawakin nan Ado Isa Gwanja.   Abdullahi Muhammad mai shekaru goma ya biyo motar gawayi daga garin Shelang har zuwa nan Kano, ba tare da sanin iyayen sa ba.   Wakilin mu Yusuf Ali Abdallah ya rawaito mana cewa, jami’an Hisba sun dakume yaron kafin ya samu ganawa da Ado Gwanja.   Gwani Murtala Mahmud shi ne kwamandan Hisbah na karamar hukumar Kumbotso ya ce, yanzu haka suna shirye-shirye domin mayar da wannan yaron zuwa ga hannun iyayen sa.   Ku kasance da shirin Inda Ranka @7am don jin yadda wannan yaro ya rerawa shirin Inda Ranka wata wakar sa.