fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: Afganistan

Yanda matashiya ‘yar shekaru 14 ta kashe ‘yan Ta’addar da suka kashe mata mahaifa

Yanda matashiya ‘yar shekaru 14 ta kashe ‘yan Ta’addar da suka kashe mata mahaifa

Uncategorized
Wata matashiya 'yar Afghanistan ta samu yabo a kafafen sada zumunta bisa gwanintar da ta nuna bayan yaƙar wasu 'yan Taliban biyu da suka kashe iyayenta.   Yarinyar ta yi amfani da bindigar gidansu ƙirar AK-47 wajen harbe mutanen tare da raunata wasu da dama, a cewar jami'ai a Lardin Ghor. Jami'an sun ƙara da cewa 'yan Taliban ɗin sun je gidan saboda mahaifin yarinyar yana goyon bayan gwamnati.   Wani hoton yarinyar riƙe da bindiga dai ya karaɗe shafukan sada zumunta a 'yan kwanakin nan.   Daga baya kuma ƙarin mayaƙa sun sake dirar mikiya a gida da ke ƙauyen Griwa amma kuma al'ummar yankin da mayaka masu samun goyon bayan gwamnati suka fatattake su.   Jami'ai sun ce tuni aka kai matashiyar da shekarunta ba su wuce tsaka...
An samu fashewar wani abu a cikin masallaci yayin sallar Juma’a wanda yayi sanadin mutuwar limami tare da jikkata mutane dadama a babban birnin Afganistan

An samu fashewar wani abu a cikin masallaci yayin sallar Juma’a wanda yayi sanadin mutuwar limami tare da jikkata mutane dadama a babban birnin Afganistan

Tsaro
Shafin Aljazeera ya rawaito cewa, an samu fashewar wani abu a cikin masallaci yayin sallar Juma'a a yammacin Kabul babban birnin kasar wanda ya kashe a kalla mutane hudu tare da jikkata wasu da dama. Rahotanni sun nuna cewa, a kalla mutane hudu, ciki har da limamin masallacin ne, suka rasa ransu yayinda wasu da dama suka jikkata, kamar yadda ma'aikatar cikin gida ta Afghanistan ta shaida. Ma'aikatar ta shaida hakan ne a cikin wata  sanarwa data fitar, inda ta bayyana cewa limamin masallacin Azizullah Mofleh na cikin wadanda suka rasa ransu a harin. Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida Tariq Arian ya ce 'yan sanda sun taimaka  wajan bada taimakon gaggawa domin ceto wadanda suka jikkta a yayin harin zuwa asbitoci mafi kusa dake yankin. Sai dai har zuwa yanzu babu wata kungiy...
Zakaran da Allah ya nufa da Chara: Jaririyar da aka harba sau 2 a harin da ISIS suka kai dakin Haihuwa a Kabul ta rayu

Zakaran da Allah ya nufa da Chara: Jaririyar da aka harba sau 2 a harin da ISIS suka kai dakin Haihuwa a Kabul ta rayu

Tsaro
A ranar Talatar data gabatane mayakan kungiyar dake ikirarin jihadi ta ISIS suka kai hari babban birnin kasar Afganistan, Kabul inda ta kashe akalla mutane 24.   Akwai jaririya wadda awanni 3 kacal da haihuwarta wadda aka harba har sau 2 a kafa yayin harin. Maharan sun shiga Asibitin, bangaren haihuwa su 3 sanye da kayan jami'an tsaro, suna shiga suka watsa ababen fashewa, aka fara batakashi dasu da jami'an tsaro. Daga karshe dai an samu kashesu saidai sunyi sanadin kashe mutane 24 ciki hadda jarirai sabuwar haihuwa 2 da mata da maza.   Mahaifiyar jaririya, Nazia da aka harba sau 2 a kafa ta rasu a sadain harin kuma tuni Likitoci suka mata aiki a kafar da aka harbeta. Mahaifin jaririyar, Rafiullah ne ya sakawa diyar rashi sunan Nazia wanda shine suna...