
“Yan kunar bakin wake sun kaiwa wani Gwamna a kasar Afghanistan hari
Harin kunar bakin wake yayi sanadin salwantar rayuka, yayin da Wani Gwamna A gabashin Afghanistan ya tsallake rijiya da baya
Rahotanni daga kasar Afghanistan na cewa, A kalla mutane Jami'a 4 da mutanan gari ne su ka rasa rayukan su, yayin da mutane 38 su ka jikkata, a wani harin kunar bakin wake da a ka kai kan Jerin gwanon gwamnan lardin Rahmatullah Yarmal lokacin da ayarin motocin sa, ke wucewa ta yankin Sultan Ghazi Baba, dake garin Mehtarlam, babban birnin kasar, A gabashin Laghman a ranar Litinin.
Wasu Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin da wata mota wanda yayi sanadin salwantar rayuka.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan ya tsallake rijaya da baya, yayin da yake cikin wata mota mai sulke.
A wata Sanarwa da aka fitar, an zargi kun...