
Hotuna: Soja ya dirkawa wani matashi harsashi saboda bai saka takunkumin rufe baki da hanci ba
Wani soja a kasar Yankin Mogwadi, Limpopo dake kasar Africa ta kudu ya dirkawa wani matashi, dan shekaru 27 harsashi yayin da gaddama ta kaure tsakanin akan dalilin da yasa matashin bai saka takunkumin rufe baki da hanci ba.
Kakakin 'yansanda, Motlafela Mojafole ya bayyana cewa lamarin ya farune ranar 17 ga watan Satuma, watau, Jiya kenan.
Yace am kama sojan inda ake zarginsa da kisan ganganci yayin da shi kuma wanda aka harba din aka garzaya dashi Asibiti.