
Mane ya taimakawa Senegal ta zama kasa ta farko data cancanci buga gasar cin kofin Nahiyar Africa
Dan Kwallon kafar kasar Senegal me bugawa kungiyar Liverpool wasa, Sadio Mane ya taimakawa kasarsa da kwallo wadda suka samu nasara akan Guinea Bissau da 2-0.
Da wannan nasara, Senegal ta samu kaiwa ga buga gasar Cin kofin Nahiyar Africa a 2022.
A mintuna 82 ne Mane ya saka kwallon data basu nasara wanda a yanzu suna da maki 12 kenan.