
Akwai Wasu mutane dake Amfana da ayyukan ‘yan Bindiga>>Kakakin Majalisa, Sanata Ahmad Lawal
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya dage kan cewa wasu mutane na cin gajiyar ayyukan yan bindiga a Najeriya.
Lawan ya yi magana bayan tabbatar da shugabannin hafsoshin tsaro.
Ya koka kan yadda ayyukan 'yan fashi ke zama wata masana'anta a kasar nan.
Shugaban majalisar dattijan wanda ya bukaci shugabannin rundunonin da su kawo karshen wannan mummunan halin, ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba.
Lawan ya ce, “Yanayin da wasu gungun mutane za su tafi makaranta su tafi da dalibai dari uku a kan babura ba abin yarda bane.
“Satar mutane ba tare da wata alama ba, ba abar karba ce. Dole ne a yi wani abu saboda, a bayyane yake, wannan ya zama masana'anta, wasu mutane suna cin gajiyar wannan, kuma dole ne mu fayyace ko su wanene mutanen kuma mu...