
Muna tuya Ana mantawa da Albasa: Kamata yayi a nemi wanda yawa Annabi(SAW) Batanci a hukuntashi>>Ahmad Shanawa
Tauraron mawakin Hausa, Ahmad Shanawa yayi martani akan batancin da akawa Annabi(SAW) bayan da tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau ta saka wasu hotuna da suka dauki hankula a shafukan sada zumunta.
Ahmad Shanawa a wani Bidiyo da ya saka a shafinsa na Instagram ya bayyana cewa, kamata yayi a yi bincike dan gano inda wanda yayi batancin yake dan a dauki mataki akansa.
Ya bayyana cewa ya kamata a kamoshi a hukuntashi dan ya zama darasi ga 'yan baya.
https://youtu.be/dPx7an5vInk
https://www.instagram.com/p/CHKxu9TpbG7/?igshid=1vb3wmncegyqw