
Shugaba Buhari ya baiwa ma’aikatan Najeriya tabbacin cewa babu wanda za’a kora daga aiki ba tare da bin ka’idoji da suka dace ba
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a sakon ranar ma'aikata, ya tabbatarwa da ma'aikatan cewa babu wanda za'a kora ba tare da bin ka'idojin da suka dace ba.
Shugaban wanda Ministan kwadajo, Chris Ngige ya wakilta a ganawar da suka yi da wakilan kungiyar kwadago ta fasahar zamani, kamar yanda me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya tabbar yace yasan akwai fargabar dake tattare da ma'aikatan kan ayyukansu, musamman a wannan hali da ake ciki na Annobar cutar Coronavirus/COVID-19.
Saidai yace su kwantar da hankalinsu babu wanda za'a kora daga aiki, musamman ma daga bangaren kamfanoni masu zaman kansu ba tare da bin ka'idojin da suka dace ba.
Yace dolene sai an tattauna da ma'aikatan da wakilansu da kuma hukumomin da suka kamata.
Sa...