fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Aikin Hajji

Yanda ‘Za ku fara tanadin kuɗin aikin Hajji da naira 1000’

Yanda ‘Za ku fara tanadin kuɗin aikin Hajji da naira 1000’

Uncategorized
Hukumar alhazai ta Najeriya ta fito da bayanai game da sabon tsarinta na adashen gata ga dukkan masu buƙatar zuwa Hajji a nan gaba ta hanyar biyan kuɗin kujera da kaɗan-kaɗan.   Ta wannan tsari ne hukumar ta saka hannu kan wata jarjejeniya da Bankin Jaiz a Abuja babban birnin tarayyar ƙasar. Dakta Aliyu Tanko, shi ne jagoran wannan sabon tsari na adashen gata a hukumar alhazai ta Najeriya, inda ya ce wannan tsarin wata hanya ce ta buɗe wa duk wanda yake Musulmi, ko talaka ko mai kuɗi domin zuwa aikin Hajji.   "Wannan tsari ne da zai bayar da dama ga mutum ya rinƙa ajiye kuɗi a hankali, mai dubu ɗaya ya je ya ajiye, mai dubu biyar ya je ya ajiye, wanda ke da dubu goma shi ma ya je ya ajiye," in ji Dakta Aliyu.   "Wannan kuɗin da kowa ya ajiy...
Mahajjatan Najeriya sun ki karbar kudin aikin Hajjinsu da basu samu zuwa ba>>NAHCON

Mahajjatan Najeriya sun ki karbar kudin aikin Hajjinsu da basu samu zuwa ba>>NAHCON

Uncategorized
Shugaban hukumar Hajji ta kasa, NHCONA, Alhaji Sirikullah Kunle Sanni ya bayyana cewa kaso 90 cikin 100 na Mahajjatan Najeriya da basu samu zuwa aikin hajjin ba sun ki yadda su karbi kudadensu da suka biya.   Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Kwara. Inda yace kaso 10 ne kawai suka karbi kudaden hajjin nasu amma sauran na hannun hukumar. Yace bai san ko nawane zasu cika ba dan yin aikin hajjin bana. Yace duka kudaden Mahajjatan suna ajiyene a wajan babban bankin Najeriya, CBN.
Aikin Hajjin Bana sai mai Rabo

Aikin Hajjin Bana sai mai Rabo

Uncategorized
Ƙasa da mako guda a fara gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki, Hukumomin Saudiyya na ci gaba da shirye-shirye don aiwatar da wannan muhimmiyar ibada bana.   Mutum 10,000 ne kawai za su yi ibadar a bana, kuma waɗanda ke zaune a Saudiyya kawai, ciki har da 'yan ƙasar da kuma wasu da suke je Saudiyyan daga ƙetare.   An rage yawan masu zuwa ibadar aikin Hajjin ne saboda annobar korona wadda ta addabi al'ummar duniya.   Wani dan Najeriya mazaunin birnin Madina, Muhammad Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa ko da yake al'amura sun fara kankama, amma babu hada-hada kamar yadda suka saba gani a shekarun baya.   Ya dai musanta raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa cewa kafin a zaɓi mutumin da ya dace don gudanar da Hajjin bana sai ya yi rantsuwa cewa...
Rukunin farko na alhazai ya isa birnin Jeddah

Rukunin farko na alhazai ya isa birnin Jeddah

Uncategorized
Rukunin farko na alhazai ya sauka a filin jirgi saman Sarki Abdulaziz da ke Jedda inda za su dauki aniyar gudanar da aikin Hajjin bana. Sakon da shafin Twitter na Haramain ya wallafa, ya nuna jami'an suna tarbar maniyyatan a yayin da suke bin tsarin kula da lafiya domin kauce wa kamuwa da cutar korona. "Rukunin farko na mahajjata ya isa filin jirgin saman Sarki Abdulaziz na kasashen duniya da safiyar yau, inda jami'ai suka tarbe su cikin daukar tsarin kariya",a cewar sakon. A watan Yuni ne mahukuntan Saudiyya suka ce mazauna kasar ne kadai - cikinsu har da 'yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta - za a bari su yi aikin Hajjin bana. Mutum 10,000 ne kawai za su yi aikin hajjin bana amma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da 'yan wasu kasashen da ke zama a can. Sai dai ...
Gwamnan Jihar Sokoto Ya Bada Umarnin Maidawa Maniyyata Hajji kudadensu

Gwamnan Jihar Sokoto Ya Bada Umarnin Maidawa Maniyyata Hajji kudadensu

Siyasa
Gwamnatin Jihar Sokoto ta umarci a mayar wa maniyyata aikin Hajjin 2020 kudaden kujeru da suka biya bayan kasar Saudiyya ta soke aikin saboda bullar cutar annobar korona. Hukumar alhazan jihar, bayan samun umarnin daga Gwamna Aminu Tambuwal, ta ce ta fara shirin mayar wa maniyyatan kudadensu nan ba da jumawa ba. Kakakin hukumar, Shehu Muhammad Dange ya ce, “Mun umarci kananan hukumomi su tattara bayanan alhazansu domin a fara biyan su saboda kada a samu matsala”. Kakakin ya ce za a mayar da kudaden bisa tsarin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), “ko da yake wasu za su so a ci gaba da ajiye kudadensu har zuwa lokacin aikin Hajjin 2021. Ya shawarci maniyyatan da su dauki rashin samun halartar ibadar ta bana a matsayin kaddara. Saudiyya ta dakatar da halartar aikin Hajjin...
Sharudan Aikin Hajji Na Wannan Shekarar

Sharudan Aikin Hajji Na Wannan Shekarar

Uncategorized
Gwamnatin Saudi Arabia ta fitar da sharuda 6 gabanin aikin hajjin wannan shekarar.   A cewar ministan harkokin lafiyan kasar, Tawfiq Al-Rabiah wadanda ba su kai shekara 65 ne ba kawai za su Iya gudanar da aikin na Hajj.   Wadanda ke fama da wasu cututtuka masu tsanani ma ba za su Iya gudanar da aikin ba.   Hakan na zuwa kwana 1 bayan da hukukomi a kasar su ka bayyana cewa 'yan kasashen wane ba za su iya zuwa aikin hajjin bana ba, sai wadanda ke zaune a cikin Saudiyyar.   Duk wadanda zasu zo hajjin kuma, sai an gudanar da gwajin cutar Coronavirus a kansa kafin a basu damar shiga masalatan.   Ministan ya kara da cewa, dole sai mahajjatan sun bar tazara a tsakaninsu, kuma ana ganin cewa ba za a wuce baiwa mahajjata 10,000 damar gudanar da...
Hajj a Saudiyya: Mazauna kasar ne kaɗai za su yi aiki bana

Hajj a Saudiyya: Mazauna kasar ne kaɗai za su yi aiki bana

Uncategorized
Mahukuntan Saudiyya sun ce mazauna kasar ne kadai - cikinsu har da 'yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta - za a bari su yi aikin Hajjin bana.   Cikin wata sanarwa da ma'aikatar aikin Hajji kasar ta fitar ta ce sun dauki mataki ne bisa la'akari da yadda cutar korona ta yadu zuwa kasahe sama da 180 a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar da wadanda ke dauke da ita da suka kai miliyan bakwai a fadin duniya. Ga rashin riga-kafin annobar da ake fama da ita a duniya da kuma bukatar tabbatar da tazara tsakanin mutane da hana taron jama'a duka wadannan na daga cikin dalilan da ya sa aka soke Umara a bana, in ji sanarwar.   Sanarwa ta kara da cewa yadda cutar ke ci gaba da yaduwa da kuma yadda aka gaza samar da wata mafita in ba tabbat...
Akwai yiyuwar za’a yi aikin hajjin bana>>NAHCON

Akwai yiyuwar za’a yi aikin hajjin bana>>NAHCON

Siyasa
Hukumar aikin hajji ta Najeriya, NAHCON ta bayyana cewa tana jiran kasar Saudiyyane ta fitar da sanarwa kan ko za'a yi aikin hajjin bana ko kuwa a'a.   Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana haka a wata ganawa ta yanar gizo da ya halarta. Yace duk da annobar cutar Coronavirus/COVID-19 amma alamu na nun cewa watakila ayi aikin hajjin bana na 2020 saboda lura da irin matakan da kasar Saudiyya ke dauka.   Ya kara da cewa, saidai suna tsammanin aikin hajjin na bana zai zo da tsauraran matakai cikin hadda ragewa kasashe yawan mahajjata.