
Yawan wanda basu da aikin yi sun karu zuwa miliyan 23.18 a Najeriya>>NBS
Sama da 'yan Nijeriya miliyan 23.18 ba su da aikin komai ba ko kuma suna aiki na kasa da awanni 20 a kowanne mako, wadda hakan ke nufin ba su da ayyukan yayin watanni hudu na karshen shekarar 2020, kamar yadda Jaridar The Cable ta ruwaito.
A cewar rahoton kan rashin ayyukan yi da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) da ta fitar a ranar Litinin, hakan na nufin kashi 33.3 na cikin 100 na masu neman aiki a Nijeriya ba su da ayyukan yi a shekarar 2020 daga kashi 27.1 cikin 100 a zango na biyu na shekarar 2020.
A lokacin, duk da cewa rashin aikin yi ya ragu daga kashi 28.6 zuwa 22.8 cikin 100, alkalluman rashin aikin yi da rashin samun kwakwarar aikin yi ya kai kashi 56.1 cikin 100.