fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Akwa Ibom

Rikicin Kabilanci yayi sanadin salwantar rayukan mutum 7 a jihar Akwa Ibom

Rikicin Kabilanci yayi sanadin salwantar rayukan mutum 7 a jihar Akwa Ibom

Uncategorized
Fiye da mutane bakwai rahotanni suka tabbatar da cewa an kashe yayin da mutane da yawa suka jikkata a wani rikicin kabilanci tsakanin Al'umomin Uko Ntenghe da Uko Akpan dake karamar hukumar Mbo na jihar Akwa Ibom. Al’umomin biyu da suka kwashe shekaru suna takaddama kan filayen noma, sun sake tayar da rikicin ne a ranar Litinin lokacin da wasu matasa da ake zargin ‘yan asalin kauyen Uko Ntenghe ne, garin mahaifar Sakataren Gwamnatin Jiha, Dakta Emmanuel Ekuwem, inda ake zargin su da yiwa wata fyade a wata gona dake Uko Akpan. Kauyen Uko Akpan, abin birgewa, shi ne garin tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda na kasa (IGP) marigayi Etim Inyang. Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce wasu matasa daga Uko Ntenghe sun shiga Uko Akpan a Enwang, hedkwatar karamar hukumar Mbo, inda s...
Rundunar hadin gwiwa ta cafke buhunan Shinkafa 800 tare da yin barazanar kona dakin ajiyar ‘yan fasa-kwauri a Akwa Ibom

Rundunar hadin gwiwa ta cafke buhunan Shinkafa 800 tare da yin barazanar kona dakin ajiyar ‘yan fasa-kwauri a Akwa Ibom

Tsaro
Rundunar hadin gwiwa, wacce ta hada da Hukumar Kwastam ta Najeriya, da Sojoji, da DSS da kuma ’Yan sanda, sun cafke buhunan shinkafar sumogal 800 daga rumbunan adana kaya a Unyenghe, da ke karamar Hukumar Mbo, ta Jihar Akwa Ibom. Rundunar ta ayyukan kan iyaka, karkashin jagorancin Kwanturolan Kwastam din da kuma Kodinetan sashen na Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma, Mista Shehu Abubakar, ya kuma yi barazanar kona rumbunan ajiyar masu fasa-kauri a yankin idan ba su daina ayyukan su na haram ba. Da yake magana da manema labarai a ranar Lahadi bayan harin, Abubakar ya bayyana yankin a matsayin matattarar masu fasa-kwauri, yankin jin dadi da kuma garin shinkafa da aka gano ta hanyar bayanan sirri. Ya ce atisayen shi ne na farko a yankin bayan shekaru masu yawa, yana mai lura da ce...
Jihar Akwa-Ibom ma ta saka ranar 21 ga wata dan bude makarantunta

Jihar Akwa-Ibom ma ta saka ranar 21 ga wata dan bude makarantunta

Siyasa, Uncategorized
Jihar Akwa-Ibom ta saka ranar 21 ga watan Satumba a matsayin ranar da za'a bude makarantun gaba da sakandare na jihar. Hakanan ta saka ranar 28 ga watan a matsayin ranar da za'a bude makarantun Firamare da na Kimiyya da fasaha na jihar. Kwamishinan yada labarai na jihar Ini Ememobong ne ya bayyanawa manema labarai haka ranar Juma'a a Uyo.   Yace aji 6 na Firamare ne kawai zasu koma ci gaba da karatu dan shiryawa jarabawar fita sannan dolene a bi dokokin kare yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.
‘Yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kama dan wani fasto da laifin yi wa wata yarinya‘ yar shekara biyar fyade

‘Yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kama dan wani fasto da laifin yi wa wata yarinya‘ yar shekara biyar fyade

Kiwon Lafiya
Wanda ake zargin mai suna Victor Felix Ukpong, mai kimanin shekaru 29, an zarge shi da haikewa wata yarinya mai shekaru 5  a cikin dakin kwanansa a wani Gida mai lamba 28 dake (Okon Dan Street) a karamar Hukumar Abak, a Jihar Akwa Ibom. A cewar Rahotan da rundunar 'yan sanda ta bayyana a ranar Asabar da cewa, "Mahaifiyar yarinyar ta bar 'yar tata ne a gidan faston gun Iyalan sa, domin taje kasuwa, wanda hakan ya baiwa Ukpong damar aikata mugun aniyarsa akan 'yar karamar yarinya. Sai dai Rundunar 'yan sanda ta sakaya sunan Mahaifin Matashin wanda aka bayyana shi a matsayin limamin coci. A cewar Kakakin ‘yan sanda a jihar, N-nudam Fredrick, ya bayyana cewa Rundunar tai nasarar cafke Ukpong a ranar 2 ga watan Yuli.  Rundunar tai Ikrarin cewa zata sa kafar wando daya da duk wani ma...