
Masassarar Aladu ta kashe Aladu kusan Miliyan 1 a Najeriya
Wata Masassarar Aladu da akewa lakabi da ASF ta yi sanadin Ajalin Aladu kusan Miliyan 1 a Najeriya.
Saidai wani abin farin ciki game da wannan masassara itace bata kama dan adam. Dubunnan Aladune aka yanda a gonakin da ake kiwonsu bayan da suka kamu da cutar.
Hakan yasa masana'antar kiwon Aladu a Najeriya ta yi asarar Naira Biliyan 20 wanda hakan ya saka ayyukan mutane Dubu 20 cikin hadari.
Wannan lamari dai na zuwane a kwanakin da ake fama da cutar Coronavirus/COVID-19. Cutar ta fara a jihar Legas da Ogun wadda kuma ta watsu zuwa wasu karin jihohin Najeriya.