
Aminu Dantata ya baiwa gwamnatin Kano gudummuwar Miliyan 300 a tallafawa jama’a
Attajirin dan kasuwa a Kano,Alhaji Aminu Dogo Dantata ya bayar da gudummuwar Naira Miliyan 300 ga gwamnatin jihar dan ta yaki cutar Coronavirus/COVID-19.
Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin neman tallafin yaki da cutar ta Coronavirus/COVID-19 dan samun abinda za'a tallafawa marasa karfi dashi.
https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1244701100214816773?s=19
Kuma tuni masu kudi da kamfanoni suka fara bayar da hadin kai kan wannan lamari.
Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ne ya bayyana wannan kudi da Dantata ya bayar.