fbpx
Monday, October 26
Shadow

Tag: ali jita

Nan Gwamnati tace zata gina Fim Village mutane suka yi caaaa aka hana amma yanzu zagin ‘yan Fim ake dan basu fito zanga-zanga ba>>Ali Jita

Nan Gwamnati tace zata gina Fim Village mutane suka yi caaaa aka hana amma yanzu zagin ‘yan Fim ake dan basu fito zanga-zanga ba>>Ali Jita

Siyasa
Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita wanda yana daya daga cikin kalilan daga masana'antar Kannywood da suka fito zanga-zangar koke kan matsalar tsaro a Arewa ya bayyana cewa har yanzu Arewa bacci take.   Jita ya bayyana hakane a wani bayani da yayi kai tsaye ta shafinsa na Instagram wanda wakilin hutudole ya bibiya inda yace tun mawakan da ,irin su Shata sun yi wakar cewa "ku tashi ku farka 'yan Arewa, kusan bacci aikin kawai ne"   Yace amma har yanzu ba'a farka ba. Jita yayi kiran cewa ya kamata a farka, " An bar Arewa a baya sosai, kudu sun bar Arewa, kamin mu kamasu zamu dauki lokaci me tsawo. Wannan abu dake faruwa ya shafi kowa, wani shi a Arewa idan dai abu ba a gidansu yake ba, kai wani ma ko da a gidansu ake abu idan ba a dakinsu bane to babu ruwansa"  ...
Hotuna: A karo na 2, Ali Jita ya sake fitowa zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe-kashen Arewa

Hotuna: A karo na 2, Ali Jita ya sake fitowa zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe-kashen Arewa

Nishaɗi
Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita wanda a baya ya fito zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe-kashen da ake yi a Arewa kuma har aka kai musu hari, ya sake fitowa a yau.   Jita tare da wasu matasa sun fito dauke da kwalaye masu rubutun dake nuna bukatar kawo karshen matsalar tsaro a Arewa.   Ya saka hotunan a shafinsa na sada zumunta kamar haka: https://www.instagram.com/p/CGc1P_6AWL8/?igshid=1pb8ctecisjr9  
Muna nan muma muna shirin yanda zamu bullowa lamarin Arewa, Muna fatan zaku bamu hadin kai>>Ali Jita

Muna nan muma muna shirin yanda zamu bullowa lamarin Arewa, Muna fatan zaku bamu hadin kai>>Ali Jita

Siyasa
Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita ya bayyana cewa suna nan suma a matsayinsu na sanannu a Arewa suna shirij yanda za'a bullowa lamarin matsalolin Arewa.   Yace yasan mutane na maganar cewa a lokacin  da ake yakin neman zaben sun fito sun jawo hankulan mutane, to yanzu ma da ake cikin matsala ya kamata ace sun sake yin magana.   Yace indai 'yan kudu zasu fito cikin kwanaki 3 kacal a kuma biya musu bukatunsu to Arewa ma zamu iya jawo hankalin gwamnati, ta hanyar kiraye-kiraye ko kuma zanga-zangar Lumana.   Ali jita ya bayyana cewa ba dan kudi suka yi wannan gwanatin ba. Ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram inda ya kara da cewa akwai inda aka kirasu za'a basu kudi amma dan sunawa wannan gwamnati kyakkyawan zato suka goyi bayanta. https://www.instag
Sabuwar Wakar Ali Jita ta Call on Me

Sabuwar Wakar Ali Jita ta Call on Me

Nishaɗi
Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita ya saki wata sabuwar waka da yawa taken Call on Me.   Jita ya saki wakar ta soyayya ta shafinsa na sada zumunta wadda yayi amfani da Ingausa wajan rera ta.   Tuni dai Masoyansa suka fara nuna son wakar. https://www.instagram.com/p/CGB3Gd5Ag6s/?igshid=1w2aeywknmqlu   https://m.youtube.com/watch?v=iIw4ut_JW04
Duk wanda bai iya cinye abinda ya tara ya aiko mana>>Martanin Ali Jita kan ikirarin tashin Duniya

Duk wanda bai iya cinye abinda ya tara ya aiko mana>>Martanin Ali Jita kan ikirarin tashin Duniya

Nishaɗi
A dazu ne mukanji cewa wani matashi daga Kaduna yayi ikirarin cewa wai Duniya zata tashi tsakanin watan Disamba da Janairu.   Tauraron mawakin Hausa,  Ali Jita ya bayyana cewa, abokin aikinsa, El-Muaz ya aika masa da wannan sako inda matashin ke cewa kowa ya cinye abinda ya tara.   Saidai Jita yace shi idan baku iya cinye abinda kuka tara to ku aika masa. https://www.instagram.com/p/CFrN5nzgjdl/?igshid=1ebjbn2y9iocb   https://youtu.be/Q7L4Zjrhz6Y
Kana jiran taka ni tawa ta Iso>>Ali Jita ya gayawa Nazir Sarkin Waka kan motar Naira Miliyan 65 da aka masa Alkawari

Kana jiran taka ni tawa ta Iso>>Ali Jita ya gayawa Nazir Sarkin Waka kan motar Naira Miliyan 65 da aka masa Alkawari

Nishaɗi
A jiya ne dai muka kawo muku cewa taurarin mawakin Hausa kuma jarumin fina-finan Hausa, Nazir Ahmad Sarkin ya samu kyautar motar alfarma ta G-Wagon 2019.   Hakana mun kawo muku cewa shafin Cars na kasar Amurka yace motar na kaiwa akalla Naira Miliyan 65.   Saidai a yayin da wasi ke bayyana mamakin an yiwa Nazir sarkin waka kyautar Motar, shi kuwa abokin aikin Nazir, Watau Ali Jita, Me makogoron zinare, Kamar yanda Baba Ari ya masa kirari, ya bayyana cewa shi tasa G-Wagon din ta karaso.   Jita ya saka hoton Motar a shafinsa na Instagram inda ya bayyanawa Nazir cewa a yayin da yake jiran tasa, shi kuma gashi tashi ta karaso. https://www.instagram.com/p/CFKExyBg1sP/?igshid=2v9h7gkqjmy9
Hotuna:Ali Jita ya budewa Matarsa Asibiti

Hotuna:Ali Jita ya budewa Matarsa Asibiti

Nishaɗi
Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita ya sanar da budewa matarsa, Asibiti a Kano.   Jita ya bayyana cewa Asibitin shine burin matarsa shiyasa yayi kokarin ganin ya bude mata shi. A sakon da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Jita ya bayyana cewa yana godiya ga duka wanda suka je dan tayashi Murna.   https://www.instagram.com/p/CFGwO7Sg1VK/?igshid=2ujex4pbkrgc  
Ali Jita na gyaran Naman Layyarsa

Ali Jita na gyaran Naman Layyarsa

Nishaɗi
Tauraron Mawakin Hausa, Ali Isa Jita kenan a wannan hoton yayin da yake gyaran Naman Sallarsa.   Ya sakawa Masoyansa hoton a shafukan sada zumunta inda ya mai taken "Sarkin Pawa, Barkan Mu da Sallah" https://www.instagram.com/p/CDWMQZ9Azck/?igshid=2yhs3grxgjyq
Kayatattun hotunan Ali Jita yana bikin Murnar zagayowar ranar haihuwarsa da iyalinshi

Kayatattun hotunan Ali Jita yana bikin Murnar zagayowar ranar haihuwarsa da iyalinshi

Nishaɗi
Tauraron mawakin Hausa,  Ali Jita kenan a wadannan hotunan inda yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi tare da iyalinshi.   Ya bayyana farin ciki ta kuma godiya ga wadanda suka tayashi murnar wannan rana.   Ya saka kayatattun hotunan a shafinshi na sada zumunta inda aka gansu suna nishadi. https://www.instagram.com/p/CCvKtWQATXp/?igshid=175btot4dtinr