
Boko Haram Sun Kaiwa Tawagar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Mummunan Hari
INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN
Dazun nan Boko Haram suka kaddamar da mummunan harin ta'addanci akan tawagar tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff lokacin da suke rakiyar tawagar tsohon gwamnan daga Abuja zuwa garin Maiduguri don yin jana'izar mahaifinsa da ya rasu, sai Boko Haram suka kaddamar musu da mummunan hari a daidai garin Auno dake kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
'Yan ta'addan sun hallaka wasu jami'an 'yan sanda masu bada kariya na musamman Special Protection Unit (SPU) rundina ta 12 kuma harin ya rutsa da fararen hula, gawarwakinsu yana asibitin kwararru na garin Maiduguri.
Wadanda suka samu shahada Insha Allah a wannan mummunan hari sune Cpl Mustapha Yunusa, Cpl Abubakar Idris, sannan 'yan ta'addan sun taf...