fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Ali Ndume

Ya kamata Shugaba Buhari ya canja Ministocin da basa aiki yanda ya kamata>>Sanata Ali Ndume

Ya kamata Shugaba Buhari ya canja Ministocin da basa aiki yanda ya kamata>>Sanata Ali Ndume

Siyasa
Sanata Ali Ndume ya baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawarar cewa ya kamata ya mace gurbin Ministocin da basa aiki yanda ya kamata.   Sanata Ndume wanda ke wakiltar jihar Borno a majalisar dattijai sanna kuma shine shugaban kwamitin Sojoji ya bayyana cewa kamar yanda aka canja shuwagabannin tsaro haka ya kamata a duba Ministocin da basa aiki yanda ya kamata a Canjasu. Just as the President rejigged his Service chiefs, he should also reshuffle his cabinet so that non-performing ministers can be replaced with those that will implement the policies and programmes of the Federal Government faithfully.
Boko Haram na tare hanya su rika karbar kudi a hannun mutane>>Sanata

Boko Haram na tare hanya su rika karbar kudi a hannun mutane>>Sanata

Tsaro
Sanata Ali Ndume wanda shine shugaban kwamitin Sojoji na majalisar Dattijai, ya bayyana cewa Boko Haram na tare hanya su rika karbar kudi a hannun mutane.   Yayi maganane akan matsalar tsaron dsta Addabi Najeriya,  Musamman jihar Borno. Ndume ya bayyana cewa sojoji a fagen daga suna raba harsashi a tsakaninsu, saboda bai isa, wasunsu basu da hular kwano dan kariya. Yace idan fa gwamnati da gaske take wajan yaki da Boko 3, cikin watanni 6 za'a iya gamawa da kungiyar.
Yan ta’adda da yan fashi suna amfani da bindigar AK49, amma Sojojin Najeriya har yanzu suna amfani da AK47>>Senata Ndume

Yan ta’adda da yan fashi suna amfani da bindigar AK49, amma Sojojin Najeriya har yanzu suna amfani da AK47>>Senata Ndume

Siyasa
Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin soji, Sanata Ali Ndume, a ranar Laraba ya ce sojojin Nijeriya suna cikin “matuka”  rashin kudade aiki daga gwamnatin Najeriya. Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kare kasafin kudin da Sojojin Najeriya suka yi a Majalisar Tarayya, Ndume ya ce ’yan bindiga sun fi Sojoji kayan aiki. Ndume wanda ke wakiltar Kudancin Borno  ya kammala rangadin duba wasu rundunonin Sojoji a duk fadin kasar tare da Kwamitin sa kan Sojoji. Dan majalisar ya lura da cewa “Bambancin da ke tsakanin sojojin Najeriya da‘ yan fashin shi ne, su (Sojojin) an horar da su sannan kuma sun sanya kaki. "Wasu daga cikin 'yan fashin suna aiki da AK49, sabbin AKs, yayin da Sojoji ke amfani da AK47". Ya ce hatta ‘yan fashin sun kirkiro hanyoyin samun kak...
Sanata Ali Ndume naso a ragewa ma’aikatan Gwamnati Albashi

Sanata Ali Ndume naso a ragewa ma’aikatan Gwamnati Albashi

Siyasa
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta rage albashin ma'aikatan da basa zuwa aiki dalilin cutar Coronavirus/COVID-19.   Sanata Ndume wanda shine shugaban kwamitin majalisar Dattijai dake kula da harkar soji ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai a jiya,Litinin a Borno. Yace duk da matsalar da cutar Coronavirus/COVID-19 ta kawo amma jihohi da gwamnatin tarayya nata kashe dubban kudade akan ma'aikata. Yace a ra'ayinsa kamata yayi a baiwa wadannan ma'aikata tallafi da kuma rage musu kudin Albashi.   Yace ya kamata Gwamnati ta duba kudin da take kashewa kan biyan ma'aikata da harkar yau da kullun wanda sune ke lakume kaso 70 cikin 100 na kudin kasafin kudin gwamnati.   Yace dolene ma'aikatan su yi sadaukarwa. Yace ta yaya za'...
Har yanzu banga wanda yace min ya amfana da tallafin gwamnatin tarayya ba>>Sanata Ali Ndume

Har yanzu banga wanda yace min ya amfana da tallafin gwamnatin tarayya ba>>Sanata Ali Ndume

Siyasa
Shugaban kwamitin Soji a majalisar dattijai kuma sanata me wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa yana mazabarshi amma har yanzu bai ga mutum ko guda daya gayamai cewa ya amfana da tallafin gwamnati ba.   Ndume ya fara da cewa, da farko dai yana yabawa kokarin shugaban kasa,Muhammadu Buhari,Yayi kokari sosai saboda daukar matakin gaggawa da yayi na samar da tallafi bayan zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 saboda musamman talakawa, masu hannu baka hannu kwarya, zasu shiga halin kunci.   Ya kara da cewa amma abin yakici shine wanda aka baiwa aikin rabon kayan abincin basa baiwa ainahin talakawa tallafin.   Ndume ya bayyana hakane a ganawar da yayi da jaridar Vanguard kan wannan batu.   Yace kawai suna zaune a Abujane inda suka k...
ZARGIN KARKATAR DA TALLAFIN GWAMNATI: Ka Bayyana Hujjojin Ka, Ko Ka Yi Wa Mutane Shiru, Fadar Shugaban Kasa Ga Sanata Ndume

ZARGIN KARKATAR DA TALLAFIN GWAMNATI: Ka Bayyana Hujjojin Ka, Ko Ka Yi Wa Mutane Shiru, Fadar Shugaban Kasa Ga Sanata Ndume

Siyasa
Fadar Shugaban Kasa ta maida wa sanata Ali Ndume da kakkausar martani inda ta karyata korafin da ya yi cewa ana tafka harkalla a rabon tallafin agaji da gwamnatin tarayya take baiwa ‘yan Najeriya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.     Sanata Ali Ndume ya zargi Kwamitin Rabon Kayan Tallafin Rage Radadi Lokacin Coronavirus, wanda ke karkashin Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Umar, da tabka almundahana, harkalla da rub-da-ciki.     Ndume, wanda ke wakiltar Mazabar Sanatan Barno ta Kudu, ya ce idan dai ba Shugaba Muhammadu Buhari ya na so a kifar masa da dan sauran kima da mutuncin sa da suka rage a cikin yashi ba, to ya gaggauta kwace rabon kudi da kayan agaji daga hannun kwamitin da Sadiya Farouq ke shugabanta. &nb...
A rusa kwamitin dake rabon kudi  gwamnatin tarayya, cin hanci hanci ya musu yawa, wanda suke baiwa kudi ba ainahin talakawa bane>>Sanata Ali Ndume

A rusa kwamitin dake rabon kudi gwamnatin tarayya, cin hanci hanci ya musu yawa, wanda suke baiwa kudi ba ainahin talakawa bane>>Sanata Ali Ndume

Siyasa
Sanata Ali Ndume wanda shine shugaban kwamitin dake kula da harkar soji a majalisar tarayya ya caccaki tsarin gwamnati  tarayya na rabon tallafin ragewa 'yan Najeriya radadin cutar Coronavirus/COVID-19.   Yayi wannan caccakane a Borno yayin ganawa da 'yan Jarida.   Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, a rusa kwamitin dan cin hanci ya musu yawa yawa yace wanda ake baiwa kudin tallafin ba sune suka cancanta ba, sannan jihohin da suka cancanci samun kudin ba can ake kaiwaba.   Yace musali a jihar Borno,Rijistar SIP ta nuna cewa akwai mutane 33, 748 da suka cancanci samun kudin,yace wannan shirmene, ,an iya samun wadannan mutanen a mazabar Mari.   Ya kara da cewa yana da labari daga majiya me karfi cewa, rijistar da kwamitin ke amfani da ita ta karyace, w...