
Manajan Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana cewa Alisson zai dauki tsawon makonni biyu kafin ya warke daga rauni
Babban golan Liverpool, Alisson ya rasa wasan da kungiyar ta lallasa Ajax a gasar zakarun nahiyar turai, yayin da Caoimhin Kelleher ya maye gurbin shi kuma yayi kokari sosai wanda har ya kai ga manajan kungiyar Jurgen Klopp ya yabe shi.
Jurgen Klopp ya bayyana cewa ba cutar Covid-19 ce ke damun dan wasan ba, ya fada masu ya samu rauni ne a minti na 60 zuwa 70 a wasan su da Brighton, kuma irin raunin daya samu sai ya dauki tsawon kwanaki 10 zuwa 14 kafin ya warke.
Golan Brazil din zai rasa wasan da Liverpool zata karbi bakuncin Wolves a gasar Premier league sannan kuma zai rasa wasan da Liverpool zata ziyarci Midtjylland a gasar zakarun nahiyar turai mako mai zuwa.