
Tsohon Babban Lauyan jihar Kano kuma kwamishinan shari’a Aliyu Umar, SAN ya rasu
Kwamishinan Jahar Kano, Aliyu Umar ya rasu
Tsohon Babban Lauyan jihar Kano kuma kwamishinan shari'a, Aliyu Umar, SAN ya mutu.
Ya rasu a safiyar Juma’a da misalin karfe 4:00 bayan gajeriyar rashin lafiya.
Anyi jana'izar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Kafun rasuwar sa mirgayi Aliyu Umar ya kasance fitaccen masanin shari'ar, wanda ya bada gudunmawa a harkar Shari'a.