
Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin alkalan Kotun Koli guda takwas
Majalisar dattijai a ranar Talata ta amince tare da tabbatar da nade-naden alkalan Kotun Koli guda takwas.
Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya tura wasikar da shugaban majalisar dattijan, Ahmad Lawan ya karanta, inda ya nemi majalisar ta amince da nadin alkalan takwas.
Buhari ya ce nade-naden sun dogara ne da shawarwarin da Majalisar Kula da Harkokin Shari'a ta Kasa ta bayar.
Buhari ya kuma ce matakin nasa ya kasance "bisa ga sashi na 231 (2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima kuma bisa shawarar Majalisar Kula da Harkokin Shari'a ta Kasa gwargwadon matsayinsu da kuma matsayinsu a Kotun daukaka kara."
Wadanda aka zaba sun hada da, Lawal Garba, (Arewa maso yamma), Helen Ogunwumiju (Kudu maso Yamma), Abdu Aboki ...