fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Tag: Alkalanci

An nada alkali mai sa hijabi ta farko a Birtaniya

An nada alkali mai sa hijabi ta farko a Birtaniya

Siyasa
An nada Musulma mai sanya hijabi ta farko a matsayin alkalin kotu a kasar Birtaniya.     Raffia Arshad ita ce Musulma da ke sanya hijabi ta farko da ta taba zama alkali a Birtaniya.   Sabuwar alkalin mai shekara 40 ta zama alkali a yankin Midland bayan shafe shekara 17 tana aikin sharia.     Jaridar Indepent ta ambato Raffia na shaida wa Metro cewa a baya ta dauka matsayin iyayenta da kasancewarta daga al’umma marasa rinjaye za su zama mata kalubale a fannin sharia.     “Wannan nasarar ba tawa ba ce ni kadai. Nasara ce ga dukkan mata musamman Musulmai, har ma da wadanda ba Musulmai ba,” inji ta.     Raffia ta yi alkawarin amfani da sabon matsayinta wurin yin adalci da bayar da murya ga kowane bangare...