fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Tag: Almajirai

Mafi yawan ‘Almajiri’ ba ‘yan Najeriya bane>>Gwamna Ganduje

Mafi yawan ‘Almajiri’ ba ‘yan Najeriya bane>>Gwamna Ganduje

Siyasa
Mafi yawan daliban makarantar karatun Al-Qur'ani, wanda aka fi sani da 'Almajiri', wadanda ke yawo a titunan arewacin kasar, ba 'yan Najeriya ba ne, in ji gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a ranar Litinin.   Da yawa daga cikinsu baƙi ne daga Jamhuriyar Nijar, Chadi da Kamaru,” in ji Ganduje yayin da yake bayani a Wani taro na kwana 3 da Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Duniya (UBEC) ta shirya a Kano.   Ya kara dacewa binciken da muka gudanar, ya nuna cewa mafi yawan" Almajiri "da ke yawo a titunanmu sun fito ne daga Nijar, Chadi da arewacin Kamaru.
Jihohin Arewa Zasu Cigaba Da Kwashe Almajirai Zuwa Jihohin Su Na Asali

Jihohin Arewa Zasu Cigaba Da Kwashe Almajirai Zuwa Jihohin Su Na Asali

Siyasa
Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin kasar nan suna shirin fara fitar da Alamajirai zuwa jihohinsu na asalin. Babban sakaren kungiyar gwamnonin Arewa kuma sakataren gwamnatin jihar Filato, Danladi Atu ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a Jos ranar Lahadi. Atu ya ce, "Ba mu kammala maida Almajirai daga yankin ba. Gwamnonin Arewa ba da jimawa ba zasu hadu su zabi ranar da zasu ci gaba da mayarda almajirai zuwa jihohinsu da suka fito. Amma hakan na iya kasancewa bayan hutun Sallah. "A cewar Babban Jami'in Hukumar NGF, kusan Almajirai 11,000 ne da aka maida zuwa jihohinsu na asali yayin fara aikin farko wanda ya fara a watan Mayu. Ya yi bayanin cewa an dakatar da tafiyar Almajirai na wani dan lokaci yayin bin umarnin kungiyar Shugaban kasa kan COVID-19 wa...
Majalisa ta bukaci sanya Almajirai cikin tsarin Ilimin Zamani

Majalisa ta bukaci sanya Almajirai cikin tsarin Ilimin Zamani

Uncategorized
Majalisar Dattijai ta bukaci da a saka Almajirai cikin tsarin Ilimin Boko dan maganin yanda yara Almajirai ke watangaririya a kan titunan Arewa.   Hakan ya bayyanane a zaman majalisar bisa shawarar kwamitin dake kula da ilimin bai daya na majalisar. Shugabar Kwamitin, Sanata Akon Eyakenyi ce ta bada wannan shawara inda tace Almajiran da yawanci suke a Arewa na daga cikin mutanen da zasu amfana da tsarin dokar ilimin bai daya.   Tace gwamnatin tarayya ta samo bashin sama da Miliyan 600 dan habaka ilimin yara da basu iya zuwa makaranta wanda kuma Almajiran na cikinsu.   Majalisar ta kuma amince da kudirin kafa jami'ar Sojoji a Garin Biu, Jihar Borno, bisa kudirin da shugaban kwamitin sojojin, Sanata Ali Ndume wanda ya bayyana cewa jami'ar zata kasance ...
Gwamnatin jihar Yobe na ci gaba da tuntubar manyan Malamai dan nemo hanyar zamanantar da Almajirci

Gwamnatin jihar Yobe na ci gaba da tuntubar manyan Malamai dan nemo hanyar zamanantar da Almajirci

Siyasa
Kwamitin da Gwamnan Yobe a Najeriya Mai Mala Buni ya kafa domin yi wa almajiranci kwaskwarima ya ce yana tuntubar malaman addinin Musulunci don ganin an gyara tsarin don dacewa da zamani.   Sai dai wannan mataki na gwamna Mai Mala Buni na zuwa ne yayin da wasu jihohi kamar Kano ke kokarin soke almajiranci a jihohinsu. Batun almajiranci dai ya dade yana ci wa akasarin jihohin arewa tuwo a kwarya inda da dama daga cikin gwamnatocin yankin ke kokarin samar da maslaha.   Dr Muhammad Sani Idris, shugaban kwamitin da gwamnan na Yobe ya kafa ya ce ya zuwa yanzu, sun ganawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi inda suka yi masa bayanin kudurce-kudurcen gwamnatin Yobe da bukatarsu ta gwamnati ta shigo lamarin.   A cewarsa, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi maraba da batun in...
Almajirai Dubu 35 Kaduna ta mayar garuruwansu na Asali inda ita kuma aka mayar mata da Dubu 1

Almajirai Dubu 35 Kaduna ta mayar garuruwansu na Asali inda ita kuma aka mayar mata da Dubu 1

Siyasa
Jihar Kaduna ta bayyana cewa Almajirai 35,000 ne ta mayar zuwa garuruwansu na Asali inda ita kuma aka mayar mata da sama da Dubu 1.   Kwamishiniyar jin kai da walwalar jama'a ta jihar Hajiya Hafsat Baba ce ya bayyana haka ga manema labarai inda tace jihar ta mayar da Almajirai Dubu 35 zuwa jihohinsu na asali 17 da kuma wasu kasashe Makwabta. Tace jihar Kaduna kuma an maido mata da Almajirai dama da Dubu 1. Tace wannan matakine na ganin cewa yaran un samu ilimin addini dana Boko a gaban iyayensu.   Tace da taimakon ofishin kula da yara na majalisar dinkin Duniya, UNICEF, Jihar na baiwa Almajiran da aka dawo mata dasu kulawar data kamata.   Ta bayyana cewa banda cutar Coronavirus/COVID-19 akwai kuma ciwukan dake damun wasu almajiran wanda suke so su ba...
Hotuna:Gwamnatin Kaduna ta kama Mota cike da Almajirai da suka shiga jihar daga Jihar Nasarawa

Hotuna:Gwamnatin Kaduna ta kama Mota cike da Almajirai da suka shiga jihar daga Jihar Nasarawa

Uncategorized
Ma'aikatar kula dan jinkai da walwala ta hihar Kaduna ta bayyana kama wata mota cike da Almajirai da ta kama akan Hanyar Panbegua.   Ma'aikatar ta bayyana cewa ta kama kotarce kirar Golf 3 dake cike da Almajirai 11 da wasu manyan mutane 2 wanda suka fito daga jihar Nasarawa.   Ta kara da cewa an mika almajiran Ofishin 'yansanda na Pambegua wanda kuma suka bada tabbacin daukar matakin da ya kamata. https://twitter.com/KDHSSD/status/1273578742573604866?s=19
Mudai ba zamu kori Almajirai ba, inganta karatunsu zamu yi>>Gwamnatin Sokoto

Mudai ba zamu kori Almajirai ba, inganta karatunsu zamu yi>>Gwamnatin Sokoto

Siyasa
Sabanin matsayar da gwamnonin arewacin Najeriya suka cimma ta mayar da almajirai jihohinsu na haihuwa, gwamnatin jihar Sakkwato tace ba za ta kori kowane almajiri ba.     A cewar gwamnatin za ta dai inganta tsarin na karatun alkur'ani ta yadda ba sai yara sun tafi yawon barace-barace ba.   Dr Umar Altine Mahe, shi ne sakataren kula da hukumar ilimin larabci da adinin musulunci a jihar kuma shi ya tabbatar da lamarin a hirar shi da Sashen Hausa.     "Mu bamu da niyyar korar almajiran nan, ilimi ai ilimi ne, saboda haka dole mu gyara tsarin karatun."     A baya ma ana ta daukar matakai na kyautata wa tsarin amma hakan bai hana yara fita barace-barace ba.     A wannan karon dai gwamnati ta ce, wannan sa...
Jihar Kaduna ta bada kwangilar yiwa Almajiran da aka mayar mata dinkin Sallah

Jihar Kaduna ta bada kwangilar yiwa Almajiran da aka mayar mata dinkin Sallah

Siyasa
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin yiwa Almajiran da aka mayar mata da su daga wasu jihohin Arewa dinkin Sallah. Daya daga cikin Telolin da aka baiwa wannan aiki ne ya shaidawa shafin hutudole haka inda yace an basu unarnin yin dinkin akan lokaci dan Almajiran su samu yin kwaliyar Sallah da kayan.   Jihohin Arewa sun cimma matsayar mayar da Almajirai jihohinsu na Asali dan magance matsalar Almajirci inda suka sha alwashin saka Almajiran makarantun Boko.
Mayar da Almajirai jihohinsu na Asali shine abu mafi dacewa dan kowane Yaro ya kamata ace yana gaban iyayensa>>Gwamna El-Rufai

Mayar da Almajirai jihohinsu na Asali shine abu mafi dacewa dan kowane Yaro ya kamata ace yana gaban iyayensa>>Gwamna El-Rufai

Siyasa
Duk da damuwar da wasu 'yan kasa ke nunawa game da mayar da Almajirai jihohin su na asali a wannan lokaci da ake yaki da cutar coronavirus, gwamnatin jihar Kaduna ta ce, hakan shine mafi dacewa.     Gwamnan jihar Nasiru Ahmed El-rufai wanda ya fara mayar da Almajiran dake jihar Kaduna zuwa garuruwansu ya ce, kungiyar gwamnonin Arewaci ta amince da wannan mataki. "Ya kamata ko wanne yaro ya zauna a gaban iyayensa. Kuma wannan lokacin shine daidai" in ji shi.   Wani abu dake ci gaba da jan hankalin al'umma game da mayar da Almajirai gida shine wasu daga cikin su sun kamu da cutar coronavirus, to amma El-rufai ya ce, mayar da Almajiran garuruwansu ya na da ma’ana a yanzu, saboda ta haka ne za su fi samun taimakon da ya dace.     Kwamishiniy...
Bafa zamu lamucin kwararar Almajirai daga Arewa zuwa Yankinmu ba>>Kungiyar kare muradun Yarbawa

Bafa zamu lamucin kwararar Almajirai daga Arewa zuwa Yankinmu ba>>Kungiyar kare muradun Yarbawa

Uncategorized
Itama dai kungiyar kare muradun yarbawa ta YWC ta bi sahun takwararta ta kare muradun Inyamurai inda tace bafa zata lamunci kwararar Almajirai daga Arewa zuwa jihohin Yarbawa ba.   Shugaban kungiyar, Farfesa Banji Akintoye ne ya bayyana haka a hirar da yayi da Vanguard inda yace jihohin Arewa sun farka inda suke kokarin kashe al'adar Almajiranci data samo Asali a Arewa.   Ya kara da cewa gwamnonin jihohin na Arewa na kokarin ganin sun mayar da Almajiran zuwa jihohinsu na Asali, amma Almajiran basa son komawa jihohin nasu.   Yace dan hakane suke neman kwarara zuwa jihohin Yarbawa, yace to ba zasu lamunci wannan ba. Yace Almajiran na dauke da cutar Coronavirus/COVID-19,  duk da ba dukansu ba amma wasu daga cikinsu na dauke da cutar Coronavirus/COVID-19, i...