
Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da watangaririyar da ake da Almajirai da sunan mayar dasu jihohinsu na Asali
Majalisar wakilai ta cimma matsaya kan kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da cilla-cillar da ake da Almajirai, musamman tsakanin jihohin Arewa da sunan mayar dasu jihohinsu na Asali.
Majalisar a zamanta ta bukaci shugaba Buhari daya dakatar da wannan abu saboda ya sabawa hakkin bil'adama na Almajiran da kuma hakkinsu a matsayinsu na 'yan kasa da doka ta basu damar zama duk inda suke so.
Mambar majalisar A'ishatu Dukku ce ta kawo wannan batu kuma aka tattaunashi a majalisar. Ta bayhana cewa koda yanda ake tafiya da Almajiran bai kamata ba dan ana tafiya dasune tsakar rana wanda hakan kansa su Wahala.
Majalisar ta kuma cimma matsaya akan baiwa Gwamnnoni umarnin su tabbata an saka Almajiran cikin tsarin ilimin bai daya.