
An kama wata kungiyar mutane 10 da suka kware wajan yiwa yara, Maza, hadda almajirai Fyade a jihar Taraba
A jihar Taraba an kama wasu mutane 9 tare da wani dan kasuwa wanda suka kware wajan yiwa kananan yara maza,Fyade.
Me magana da yawun 'yansandan jihar, DSP David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace nan gaba kadan zasu gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.
'Yan sintirin unguwane dai suka kama Wani Umar Isa a Jalingo a wani kango yana lalata da wani karamin yaro da bai wuce shekaru 10 ba.
Daga nanne sai aka gano mutane 10 wanda kungiya garesu da suka kware wajan lalata yara maza ciki hadda almajirai.