fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Almajirci

Tunda an baka Khalifan Tijjaniyya, yanzu kana da damar hana Bara da Almajirci>>’Yan Arewa ga Sarki Sanusi

Tunda an baka Khalifan Tijjaniyya, yanzu kana da damar hana Bara da Almajirci>>’Yan Arewa ga Sarki Sanusi

Siyasa
A jiya ne dai aka samu Rahotannin cewa an nada tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyya na Najeriya.   Bayan Nadin, Wasu 'yan Arewa sun hau shafukan sada zumunta inda suka rika kira a gareshi da yayi kokarin ganin an hana Almajirci da kuma bara.   Sun rika tuna masa cewa, a baya ya sha kira da a daina Bara da almajiranci, to yanzu ga dama ta samu a gareshi da zai yi a aikace.   Wani me suna Abubakar Hadimi ya bayyana cewa, shugabancin Tijjaniyya da Sarki Sanusi ya samu, damace Allah ya bashi ta kawo karshen Almajiranci a aikace. Ya bayyana cewa, kusan duka Almajirai ko dai 'yan Qadiriyya ko Tijjaniyya ne. Yace yana fatan zai kira iyayen wadanna yara dan su kwashesu daga kan tituna.   Ya kara da cewa, ci gaba da ma...
Jihar Gombe zata zamanantar da Almajirci

Jihar Gombe zata zamanantar da Almajirci

Uncategorized
Jihar Gombe ta bayyana cewa zata zamanantar da Almajirci inda za'a baiwa Almajiran damar yin karatun Boko.   Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Habu Dahiru ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace zasu samarwa Almajiran tsarin karatu da zai yi daidai dana zamani. Yace hakan zai basu damar samun karatu har matsayin Digiri.
Babu gudu ba ja da baya kan hana Almajirci>>Gwamnan Filato

Babu gudu ba ja da baya kan hana Almajirci>>Gwamnan Filato

Siyasa
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya bayyana cewa matakin da suka dauka na hana almajirci abune da ya kamata a yishi tuntuni.   Yace wasu da dama da suka shude sun so hana Almajircin amma matsalar itace suna so su siyasantar da lamarin ta yanda kuma suna tsoron irin sukar da za'a musu. Yace babu dokar data hana matakin da suka dauka na almajircin. Yace Almajirci hanyar neman ilimi ce kamar kowace amma ita matsalarta shine ba tsari, za'a bar yaro ba kayan sawa ba takalmi yayi ta yawo a titi, ka yi tunanin irin mutumin da zai zama nan gaba idan ya girm.   Ya kara da cewa irinsu ne ke rikidewa su koma Boko Haram.
Zamu kada ku zabe saboda hana Almajirci>>Sheikh Dahiru Bauchi da Malaman makarantun Allo ga Gwamnoni

Zamu kada ku zabe saboda hana Almajirci>>Sheikh Dahiru Bauchi da Malaman makarantun Allo ga Gwamnoni

Siyasa
Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya Shaik Dahiru Bauchi da malaman makarantun allo sun yi barazanar daukar mataki kan gwamnonin da suka hana almajirci a jihohinsu. Martanin malaman ga dokar hana karatun almajirci da gwamnonin suka yi, ya ce za su kayar da gwamnonin a zabe kuma almajirai na da ‘yancin yin addini da neman ilimi a duk inda suke so a Najeriya. “Almajirai da alarammomi na da ‘yancinsu a matsayin ‘yan Najeriya su yi addini, su kuma zauna a inda suke so kuma ba za mu lamunci duk salon tauye mana hakki da sunan dokar hana almajirci ba, ana dibar almajirai daga wata jiha zuwa wata kamar dabbobi”, inji Shaikh Dahiru. Sanarwar tasu na zuwa ne bayan gwamnonin Arewacin Najeriya sun haramta tsarin karantun da kuma bara, tare da mayar da almajiran gaban iyayensu ...
ALMAJIRI MAI HAZAKA: Yana Almajiranci Yana Yawon Gyaran Takalma

ALMAJIRI MAI HAZAKA: Yana Almajiranci Yana Yawon Gyaran Takalma

Uncategorized
A yammacin Juma'a na ci karo da wannan yaro mai suna Abba wanda ya bayyana min cewa shi Almajiri ne, amma duk ranakun Alhamis da Juma'a da babu makarantar Allo yana fita sana'ar gyaran takalma domin samun na abinci, sabulun wanka da kuma sayen kayan sa wa.     Ganin yadda yaron wanda ya bayyana min sunsan sa a matsayin Abba, yake da karanci shekaru amma yake kokarin neman na kansa kuma a matsayinsa na Almajiri, hakan ya yi matukar ba ni sha'awa, har ta kai ga sai da na sauka daga kan abin hawan da nake domin karasawa wajensa.   Yayin da na karaso wajen sa ya bayyana min cewa shi dan garin Suleja ne daga jihar Neja amma yana almajiranci a garin Mararrabar Abuja da jihar Nasarawa. Aliyu Ahmad.
Malam Tsangaya sun mayar da harkar Almajirci kamar kasuwanci>>Gwamnatin Kano

Malam Tsangaya sun mayar da harkar Almajirci kamar kasuwanci>>Gwamnatin Kano

Siyasa
Batun jigilar Almajirai a tsakanin gwamnocin arewacin najeriya na ci gaba da kara tsamin dangantaka tsakanin mamallaka makarantun tsangayu a yankin Alarammomi a Kano da kuma gwamnatin jihar.     Gwamnatin Kano ce dai ta fara jigilar almajiran zuwa jihohin Jigawa da Kaduna su kimanin dubu 2, a wani bangare na yunkurin ta na hade tsarin karatun allo dana book.     Matakin dai ya haifar da cece-kuce tsakanin gwamnonin Kano da Kaduna a hannu guda, inda a daya hannun dangantaka ta so tayi tsami tsakanin gwamnatin Jigawa da ta Kano.     A kwanakin baya dai gwamnan Kaduna Nasir Elrufa’I yayi zargin takwaransa na Kano da kara alkaluman masu dauke da cutar Korona saboda almajiran da Kanon ta mayar zuwa Kaduna.     Yanzu hak...
Rochas Okonkwo yace bai kamata a hana Almajirci ba, Ingantashi ya kamata a yi

Rochas Okonkwo yace bai kamata a hana Almajirci ba, Ingantashi ya kamata a yi

Siyasa
Tsohon gwamnan jihar Imo kuma jiho a jam'iyyar APC, Rochas Okorocha ya bayyana cewa bai kamata a hana almajirci ba.   Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a BBChausa, kamar yanda ma'aikacin BBC din,Abdulbaqi Jari ya bayyanar.   https://twitter.com/Bahaushee/status/1267448437760548870?s=19 maganar hana Almajirci dai ta jawo cece-kuce a arewacin Najeriya inda wasu ke yabawa, wasu kuwa na ganin hakan bai kamata ba.
Za Mu Rusa Duk Gwamnatin Da Ta Yi Yaki Da Almajiranci, Gargadin Kungiyar Almajirai Ga Gwamnonin Nijeriya

Za Mu Rusa Duk Gwamnatin Da Ta Yi Yaki Da Almajiranci, Gargadin Kungiyar Almajirai Ga Gwamnonin Nijeriya

Siyasa
Almajirai a fadin tarayya sun yi gargadi da babban murya ga gwamnatin tarayya da na jihohi kan yadda ake yawo da Almajirai daga jiha zuwa jiha da sunan mayar da su jihohinsu na asali, kamar yadda New Telegraph ta ruwaito.     Yayin bayyana bacin ransu, shugaban cibiyar karatun Al-Qur'ani na tarayya, Sheikh Hassan Musa, a ranar Juma'a yace "ya kamata gwamnatoci su yi hattara kan lamarin Almajirai saboda duk gwamnatin da tayi yaki da Almajiranci za ta rushe ko shakka babu.     Sheikh Musa, wanda ya bayyana hakan a taron kaddamar da cibiyar killace Almajirai dake Tudun Fulani Hajj Camp, dake Minna, babbar birnin jihar Neja, ya ce kada a manta abinda suka yiwa gwamnatin Jonathan.     Ya ce kada a manta yadda Almajiran Najeriya suka kawar...
A karshe dai: Gwamna Ganduje ya haramta Almajiranci a Kano

A karshe dai: Gwamna Ganduje ya haramta Almajiranci a Kano

Siyasa
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya Haramta Almajiranci a jihar inda yace duk almajiran da aka mayarwa Kano daga wasu jihohi a yanzu za'a sakasu cikin tsarin bayar da ilimi kyauta na jihar. Gwamnan ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai inda ya bayyana halin da ake ciki kan yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar.   Ya kara da cewa daga cikin Almajiran da aka mayarwa jihar akwai guda 28 da suka kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 kuma an killacesu inda ake basu kulawa ta musamman.   Gwamnan ya kuma taya jama'ar jihar Murna inda suka yi bikin Sallah cikin kwaciyar hankali.
Za Mu Daure Duk Mahaifin Da Ya Kai Dansa Almajiranci Da Malamin Allon Da Ya Karbi Yaron>>Gwamna El-Rufai

Za Mu Daure Duk Mahaifin Da Ya Kai Dansa Almajiranci Da Malamin Allon Da Ya Karbi Yaron>>Gwamna El-Rufai

Siyasa
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ta gargadi iyayen da ke kai yaransu Almajirci da cewa za'a yi musu daurin shekaru biyu a gidan kaso.     El-Rufa'i ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda ya ziyarci wasu Almajirai 200 da aka kawo daga jihar Nasarawa kuma ake kula da su a kwalejin gwamnati dake Kurmin Mashi, Kaduna.   Gwamnan ya kara da cewa duk Malamin Allon da ya karbi yara zai fuskanci fushin hukuma inda za'a daure shi sannan a ci shi tarar N100,000 ko N200,000 kan ko wani yaro.     Saboda haka, za mu cigaba da karban Almajirai yan asalin jihar Kaduna domin canza musu rayuwa, kula da shi tare da sanyasu a makarantu kusa da inda iyayensu ke da zama.     Za mu cigaba da hakan har sai mun kawar da Almajirci daga...