
Da Dumi-Dumi:Kotu ta daure tsohon daraktan NIMASA kan cin Biliyan 1.5
Babbar Kotun gwamnatin tarayya dake da zamanta a Legas ta daure tsohon daraktan hukumar kula da tashoshin ruwa, NIMASA, Ezekiel Agaba tsawon shekaru 7 a gidan yari.
Kotun ta daureshine bayan samunshi da laifin sace Biliyan 1.5.
Hakanan ana mai wani zargin shi da wani tsohon daraktan hukumar na cin kudi, Miliyan 687.