fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Almundahanar

Hukumar Soji ta kori janar dinnan da shekarar data gabata ya shiga Badakalar Miliyan 100

Hukumar Soji ta kori janar dinnan da shekarar data gabata ya shiga Badakalar Miliyan 100

Tsaro
Kotun Hukumar sojin Najeriya ta kori Majo Janar Hakeem Oladapo Otiki dake kula da rundunar sojin Sokoto daga aiki bayan ta sameshi da laifin almundahanar kudi.   Kotun tace za'a ragewa sojan Mukami daga Majo Janar zuwa Birgedia Janar inda za'a kuma koreshi aiki ta hanyar wulakanci da kaskanci. Saidai ai majalisar Koli ta sojin ta duba wannan hukunci dan tabbatar da shi ko kuwa akasin haka.   Hukuncin ya bukaci kudi Miliyan 135, da kudi dala 6,600, da kuma Miliyan 159 da aka kwato daga hannun janar din sojin duk a mayarwa da Hukumar Sojinsu.   Saidai Lauyansa, Bar. Israel Olorundare(SAN) ya bukaci a wa wanda yake wakilta sassauci.   Yace kamin yanzu Janar Otiki ya kasance hazikin soja da ya samu nasarori da dama a ayyukan da yawa hukumar so...