fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Alnassr

Kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya bar kungiyar sa ta Al Nassr

Kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya bar kungiyar sa ta Al Nassr

Wasanni
Kungiyar Al Nassr ta gasar Saudi Arabia ta bayyana cewa tauraron dan wasan ta na Najeriya Ahmed Musa ya bar kungiyar, yayin da dan wasan mai shekaru 28 yake burin ya cigaba da buga wasannin shi a nahihiyar turai, inda kungiyar ke cewa "Muna yi maka godiya tare da fatan nasara, tauraron dan wasan Najeriya Ahmed Musa". Ahmed Musa ya kasance kaftin din tawagar yan wasan Najeriya ta Super Eagles kuma ya koma kungiyar Al Nassr ne daga kungiyar Premier League wato Leicester City a shekara ta 2018 da kwantirakin shekaru hudu bayan an kammala buga gasar Kofin duniya. Ahmed Musa ya buga wasanni 58 a kungiyar Al Nassr inda yayi nasarar ci masu kwallaye 11 tare da ya taimaka wurin cin kwallaye 14, kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe babban kofin Saudi Arabia Diadem a kakar 2018/19 da kuma Sau...