
Kwamitin shugaban kasa kan ambaliyar ruwa da NEMA sun bada gudummawar kayayyakin tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa a shekarar 2020 a Zamfara
Ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da kula da bala’i ta jihar Zamfara ta raba kayayyakin tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa a shekarar da ta gabata a karamar hukumar Gumi ta jihar.
Kwamishinan da ke kula da Ma’aikatar, Fa’ika Ahmad ya ce kayayyakin an bada su don rage wahalar da ambaliyar da wasu bala’o’i suka haifar a shekarar 2020.
Ta ce kayayyakin an bayar da su ne daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta NEMA da kwamitin shugaban kasa kan ambaliya.
Ta yi kira ga wadanda suka ci gajiyar da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata kuma ta yi masu gargadi game da sayar da su.
Ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da kula da bala’i ta jihar Zamfara ta kuma yi kira ga dukkan mazauna jihar da su tsabtace muhallinsu, su guji zubar da shara a magudanan ruwa da yin gini ta han...