
Bidiyo: Yadda wasu ma’aurata suka tsallake rijiya da baya a dai dai lokacin da suke daukan hotunan bikin auransu a bakin teku
Lamarin dai ya faru a kasar California dake kasar Amurka inda wasu sabbin ma'aurata aka nuna su a wani hoton bidiyo a dai dai lokacin da suke daukan hotunan bikin auransu kan wasu duwatsu dake dab da teku.
A dai dai lokacin da suke daukan hotunan nasu ne, sai wata igiyar ruwa mai karfi tai ciki dasu, har cikin ruwa, yayin da sukai ta faman linkaya don tsira da ransu.
Sai dai daga bisani anyi nasarar ceto su daga mummunan yana yin da suka tsinci kansu a ciki.
https://twitter.com/LailaIjeoma/status/1278727045749649414?s=20
https://twitter.com/LailaIjeoma/status/1278727459291176960?s=20
Lamarin dai ya dauki hankula matuka.