fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Amina J. Muhammad

Ya kamata Shuwagabannin Najeriya su baiwa matasa muhimmanci>>Amina J. Muhammad

Ya kamata Shuwagabannin Najeriya su baiwa matasa muhimmanci>>Amina J. Muhammad

Siyasa
Mataimakiyar sakataren majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Muhammad ta bukaci shuwagabannin Najeriya su rike matasa a matsayin wani Jari.   Ta bayhana hakane yayin ziyarar da ta kai hedikwatar gwamnonin Najeriya a ci gaba da rangadin da take a kasashen Africa.   Kakakin kungiyar ta Gwamnoni, Abdulrazaq Bello Barkindo ya bayyana cewa, Amina na martanine akan zanga-zangar SARS da aka yi kwanannan. Da take martani kan bukatar Gwamnonin na tallafi daga majalisar, tace majalisar bata bayar da kudi kai tsaye amma tana tallafawa masu halin bayarwar su bayar. Ta yabawa gwamnonin kan yanda suka yi game da zanga-zangar ta SARS amma kuma tace bata ji dadin wasu abubuwa marasa dadi da suka faru ba.