Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya Isa Fadar Sarkin Daura Alh Umar Faruq Umar Domin yin Ta'aziyyar Hajiya Mairo Mahaifiya Ga Alh Uba Sa'idu Daura Da Amb Adamu Sa'idu Daura.
Da safiyar ranar Asabar ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya Halarci Taron Saukar Karatun Al-Qur’ani Mai Girma na Makrantar Maryam Ado Bayero (Mai Babban Daki) dake unguwar farawa a karamar hukumar Kombotso a jihar Kano.
Makarantar wacca tai bikin saukar Dalubai kimanin 40 wanda aka gudanar da bikin saukar a harabar makarantar dake unguwar Farawa.
Daga Fadar Mai Martaba Sarkin Kano Kungiyar Tallafawa Marayu Dake Gidan Kadiriyya a jihar Kano karkashin jagorancin Sheikh Kariballah Nasiru Kabara sun kaiwa Mai Martaba Sarki Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ziyara da safiyar ranar Litinin.
Hakanan Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya Halarci Taron masu ruwa da tsaki kan farfado da Masana’antun da suka durkushe a jihar Kano karkashin Jagorancin Mai Girma Gwamnan Kano Alh. Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa Dr. Nasir Yusuf Gawuna wanda ya gudana a gidan Gwamnatin jihar a ranar Litinin
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya karbi Bakuncin Mai Martaba Sarkin Sangarin Shabu, Alhaji Mahmud Umar Bwala Da Kuma Mai Martaba Sarkin Akukhe na Akiri Alhaji Umar Sulaiman Shampa Duka daga jihar Nassarawa.
Hakanan Mai martaba sarin ya karbi Bakuncin Kungiyar (Network For Woman Awareness on Drugs a fadarsa dake Masarautar Kano.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya Halarci Bikin Saukar Karatun Al'Qur'ani Mai Girima Na Makarantar Assayyada Zainab Dake Sheka Karamar Hukumar kumbotso.
Hakanan Mai martaba sarkin ya aike da sakon ta'aziyyar sa bisa rasuwar Mahaifin tsohon gwamnan Kano Dakta Rabi'u Musa kwankwaso wanda Allah yayi masa rasuwa A ranar Juma'a.
Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya Halarci Saukar Karatun Alqur’ani Mai Girma na Makarantar Ma’ahad Mahmuda Chira Littafizul Qur’an Koki. A Yammacin Jiya Alhamis wanda yayi dai dai da 10 ga watan 12 shekarar 2020.
Hakanan Mai martaba sarkin ya kai makamanciyar irin wannan ziyarar saukar karatun Al'qur'ani a ranar Laraba 9 ga watan Nuwamba na Madarasatul Ma’ahad Isah Ibrahim Arzai Dake Unguwar Kurna.
Me martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya kaiwa tsohon gwamnan Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ziyara a gidansa dake Legas.
Sarkin ya kai ziyarar ne a karshen makon da ya gabata. Saidai babu cikakken bayanin abinda suka tattauna.
(L-R) Emir of Kano, His Royal Highness Alhaji Aminu Ado Bayero, and All Progressives Congress National Leader Asiwaju Tinubu when the Emir paid a courtesy call on the APC leader at his Bourdillon, Ikoyi, Lagos home at the weekend
A ranar juma'a 23 ga watan Oktoba Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin Babban kwamishana na kasar Indiya mai suna Shri Abhay Thakur wanda ya zu Najeriya.