
Najeriya bata shirya samar da tsaro ba saboda yawan jami’an tsaro sun yi kadan>>Alan Waka
Tauraron mawakin Hausa, Aminu Alan Waka ya bayyana cewa Najeriya bata shirya samarwa mutanen ta tsaro ba lura da yawan jami'an tsaron da ake dasu.
Ala yayi wannan Rubutu ne a shafinsa na Instagram inda ya zayyano matsalolin Najeriya sanna kuma ya bayyana cewa tabarbarewa kasar yana da alaka da satar dukiyarta da ake yi.
Ala ya kuma bayyana cewa ko kusa Albashin kananan jami'an tsaro baya isasu gudanar da rayuwarsu.