
“Nayi nadamar amincewa da yan bindiga, sun yaudareni ta hanyar rantsewa da Al-qur’ani”>> Masari
Gwamnan jihar Katsina Aminu Masara ya bayyana cewa yayi nadamar amincewa da yan bindiga daya yi bayan sun rantse da Al-qur'ani.
Inda ya bayyana cewa ganin su Musulmai ne yasa su rantse da littafi mai tsarki cewa ba zasu sake aikata wani laifin banna ba.
Amma duk da haka sun ci amanarsa aun cigaba da fashi, saboda haka yanzu ba zai sake amincewa dasu ba domin su mayaudara ne kuma barayi ne.