
Na yafe maka ni banda makiyin da na rike a Zuciya>>Jonathan ya amshi tuban dan gidan tsohon shugaban kasa,Aminu Shagari
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya amshi tuban da dan gidan tsohin Shugaban kasa, Shehu Shagari watau Aminu Shagari yayi.
A jiyane muka kawo muku cewa Aminu Shagari yace yana daga cikin wanda suka raba kawunan PDP dan kada a zabi tsohon shugaban kasar. Yace amma daga baya ya gano cewa yayi kuskure.
A sakon da ya fitar ta shafinsa na Facebook, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa shi ba irin mutanen nan ne masu rike mutum a zuciya ba.
Jonathan ya bayyana cewa yayi imani duk abinda wani mutum zai masa dama can Allah ya kaddaro sai ya faru dashi, dan haka bai rike kowa a zuciya ba.
Ya jawo hankalin Aminu da yayi koyi da halin mahaifinsa na saukin kai da kyawawan halaye.
Ga sakon nasa kamar haka:
“Dear Honourable ...