fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Tag: Aminu Wali

Kotu ta Sallami Karar Tsohon Ambasada Aminu Wali daga tuhumar kudaden kamfen

Kotu ta Sallami Karar Tsohon Ambasada Aminu Wali daga tuhumar kudaden kamfen

Uncategorized
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sallami tsohon ministan harkokin kasashen waje, Aminu Wali tare da wanke shi daga zargin karbar kudin yakin neman zabe na Naira miliyan 950 daga jam'iyyar PDP a lokacin zaben shugaban kasa na 2015. Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ce ke  tuhumar Mista Wali da Mansur Ahmed da aikata laifuka uku wadanda suka hada da karbar kudin yakin neman zabe har Naira miliyan 950 da ake zargin sun karba daga Jam’iyyar PDP a shekarar 2015, lamarin da ya saba wa sashe na 1 na dokar hana safarar kudi ta 2011. Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Lewis Allagoa ya ce masu gabatar da kara sun gaza gabatar da hujjojinsu ba tare da wata tantama ba. Don haka ya sallami wadanda ake tuhumar ku...
Kutun Sauraran kara dake Jihar Kano ta sanya ranar goma ga wata a matsayin ranar da zata  yanke hukunci game da Shari’ar tsohon Ambasa Aminu Wali

Kutun Sauraran kara dake Jihar Kano ta sanya ranar goma ga wata a matsayin ranar da zata yanke hukunci game da Shari’ar tsohon Ambasa Aminu Wali

Uncategorized
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke da zamanta a jihar Kano ta sanya ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar da zata yanke hukunci a kan zargin da  Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin kasa  zagon  kasa, EFCC ta gabatar a gaban kotu kan zargin badakar kudi harkimanin Naira Miliyan  950 da take wa tsohon ministan harkokin kasashen waje Aminu Wali da tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Mansur Ahmed. EFCC ta zarge su da karbar kudi Naira miliyan N950 daga hannun jam'iyyar PDP a matsayin kudin yakin neman zabe a shekarar 2015, lamarin da hukumar EFCC ta ce ya saba wa tanadin doka. Ya zuwa yanzu kotu ta ajiye ranar 10 ga watananan domin yanke hukunci.