
Gwamnatin tarayya ta tona Asirin masu haddasa rashin tsaro a Najeriya inda ta fadi sunayensu
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kotun Duniya ta ICC da kuma kungiyar kare hakkin bil'adama da Amnesty international ne suke kara yawan matsalar tsaron da ake samu a Najeriya.
Ministan Yada labarai, Lai Muhammad ne yayi wannan zargi a ganawar da yayi da manema labarai a Legas a yau, Litinin.
Ya bayyana cewa wadannan kungiyoyi na daukewa jami'an tsaro hankali kan aikin da suke na yaki da ta'addanci.
Yace suma wadannan kungiyoyi sun zama abokan fadan Najeriya inda sukewa hukumomin tsaron barazana kan binciken take hakkin bil'adama da kuma laifukan yaki.
“The Federal Government frowns at this unbridled attempt to demoralise our security men and women as they confront the onslaught from bandits and terrorists.
“Nigeria did not join the ICC so i...