fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty ta bukaci gwamnatin tarayya data gaggauta sakin Sharif wanda ya shirya zanga zanga a jihar katsina

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty ta bukaci gwamnatin tarayya data gaggauta sakin Sharif wanda ya shirya zanga zanga a jihar katsina

Tsaro
Kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty, ta soki Gwamnatin Tarayya da kama Sharif mutumin da ya jagoranci jerin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina. Kakakin kungiyar Amnesty, Isa Sanusi, ya koka da halin da ake ciki a cikin wata sanarwa a ranar Laraba da ya fitar. Sanarwar ta ce dole ne gwamnati ta hanzarta sakin Sharif wanda shi ne shugaban kwamitin amintattun na gamayyar kungiyoyin Arewa. Wata sanarwa a ranar Laraba ta hannun Daraktan Ayyuka na kungiyar masu zanga-zangar, Aminu Adam, ta zargi ‘yan sanda da kama Sharif din bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihar. Idan zaku tuna, Daruruwan masu zanga zanga ne dai sukai tsinke zuwa fadar gwamnatin jihar katsina In da suke raira wakoki tare da kira ga Shugaba Buhari da gwamnan jihar Aminu B...