fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Amurka

Kasar Amurka ta saka Kudin jingina Dala 15,000 ga masu son zuwa ziyara daga Najeriya

Kasar Amurka ta saka Kudin jingina Dala 15,000 ga masu son zuwa ziyara daga Najeriya

Siyasa
Sabuwar dokar ta wucin gadi da za ta iya bukatar masu yawon bude ido da masu fataucin kasuwanci daga kasashen Afirka goma sha biyu, ciki har da Najeriya, su biya kudin jingina daga dala 5,000 zuwa dala 15,000 don ziyartar Amurka, zai fara aiki daga 24 ga Disamba. Sauran kasashen da dokar zata shafa su ne na kasashen Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Laberiya, Sudan, Chadi, Angola, Burundi, Djibouti da Eritrea, Afghanistan, Bhutan, Iran, Syria, Laos da Yemen suma suna cikin jerin. Dole matafiyan Najeriya su biya jingina kamar yadda wasu rukunin maziyarta ke wuce iyaka zama a kasar da kashi 10 cikin 100. Gabaɗaya, cikin 'yan Nijeriya 177,835 da suka ziyarci Amurka a cikin 2019, ƙimar da ta wuce lokacin visa a kasar ya kai tsakanin kashi 9.45 zuwa 9.88. Adadin 17,566 suka ts...
Zaben Amurka: Ni ke samun nasara amma ana son a min Rinto>>Shugaban Amurka, Trump ya koka

Zaben Amurka: Ni ke samun nasara amma ana son a min Rinto>>Shugaban Amurka, Trump ya koka

Siyasa
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya koka da cewa ana so amai kwacen nasarar da ya samu a zaben kasar Amurka.   Ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace shine ke samun nasara a zaben amma ana son ai masa Rinto. Yace ta yaya za'a ce a kada kuri'a bayan an rufe rumfar zabe? “We are up big but they are trying to steal the election. We will never let them do it. Votes cannot be cast after the polls are closed!” he tweeted.   Ana tsammanin dai Trumpnzai lashe zabe a jihohi 13 yayin da abokin takararsa, Biden zai lashe zabe a jihohi 11, kamar yanda kafafen Labaran kasar suka bayyana.   The first results are trickling in, with US media projecting wins for the Republican incumbent so far in 13 states including Indiana, Kentucky, Oklahoma, Te...
Shigowar sojojin Kasar Amurka Najeriya suka kubutar da dan kasarsu be keta hurumin mulkin Najeriya ba>>Ministan Tsaro

Shigowar sojojin Kasar Amurka Najeriya suka kubutar da dan kasarsu be keta hurumin mulkin Najeriya ba>>Ministan Tsaro

Siyasa
Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya.), ya ce aikin kubutar da dakaru na musamman na Amurka suka yi a kwanan nan a kan Najeriya ba cin zarafin ‘yancin kasar ba ne. Ya ce gwamnatin Najeriya ta ba Amurka izinin da ya dace don gudanar da aikin. Sojojin Musamman na Amurka, a karshen mako, sun yi nasarar kubutar da wani Ba’amurke da ‘yan fashi suka yi garkuwa da shi a Najeriya. A wata hira da ya yi da manema labarai jim kadan bayan ya kare kasafin kudin Ma’aikatarsa ​​a Majalisar Dattawa a ranar Talata, Ministan ya ce Najeriya ta ba Amurka izinin “a matsayin kasa mai kawance” kusan a lokacin da ta tuntubi gwamnatin. Ya yi watsi da tunanin cewa Amurka na iya keta hurumin Najeriya. Magashi ya ce kasar na yin iyakar kokarin ta tare da abin da sojoji ke da s...
Gobarar Daji tai sanadin mutuwar mutane da dama tare da lalata gidaje a kasar Amurka

Gobarar Daji tai sanadin mutuwar mutane da dama tare da lalata gidaje a kasar Amurka

Uncategorized
Mutane da dama sun mutu ya yin da dubunnan mutane su ka tsere daga muhallan su sakamakon gobarar daji da tai sanadin halaka mutane a kasar Amurka. Wata gobarar daji tai sanadin barin wasu mazauna sama da dubu 10 da ke zaune a wani yanki dake jihar California da kuma makwabantan yankin a kasar Amurka. Gwamnan jihar Kate Brown ya ce, daruruwan gidaje ne suka kone kurmus a sanadin gobarar wacca ta fansatsama gurare a yan kunan. A cewar sa, basu ta ba ganin gobara irn wannan ba a tarin jihar. Sky News ta rawaito da cewa, Masu aikin kashe gobarar sun yi iya bakin kokarin su wajan dakile yaduwar gobarar tare da kashe wutar gaba daya a sa'ilin da take ci.  
Ba fa Kiristoci kadai ake kashewa a Najeriya ba hadda Musulmai,CAN ce kawai ke shirga maka karya>>MURIC ta gayawa shugaban kasar Amurka

Ba fa Kiristoci kadai ake kashewa a Najeriya ba hadda Musulmai,CAN ce kawai ke shirga maka karya>>MURIC ta gayawa shugaban kasar Amurka

Uncategorized
Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Addinin Musulunci ta MURIC ta mayarwa da shugaban kasar Amurka, Donald Trump martani kan tambayar da yawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa me yasa yake kashe musulmai?   A sanarwar data fitar ta hannun Daraktanta, Ishaq Akintola,  MURIC tace Trump ya sani fa bawai jami'an tsaron gwamnati bane ke kashe mutane. Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a ziyarar da ya kai kasar Amurka a shekarar 2018, shugaban kasar ya sakashi a Ofis, su biyu kawai ya tambayeshi me yasa yake kashe Kiristoci a Najeriya?   MURIC ta bayyana cewa tana zargin kungiyar Kiristoci ta CAN ce ke aikawa kasashen waje wannan rahotannin karyar. Yace amma har musulmai ana kashewa a Najeriya inda Boko Haram suke kashe limamai da sarakuna da kona mada...
Kanin shugaban kasar Amurka, Robert Trump ya mutu

Kanin shugaban kasar Amurka, Robert Trump ya mutu

Siyasa
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa kanin shugaban kasar, Doland Trump watau Robert Trump ya mutu a daren jiya, Asabar.   Shugaban kasar ne da kasa ya bayyana sanarwar mutuwar kanin nasa a jiya a fadarshi. Hutudole ya samo muku cewa a Ranar Juma'ar data gabata, Trump ya je Asibiti a birnin New York inda ya duba kanin nasa suka shafe kusan mintuna 45 tare. Saidai babu wata sanarwa kan wace irin cutace ke damunshi kamon mutuwar tasa. Hutudole ya ruwaito muku cewa Trump ya bayyana kanin nasa a matsayin babban aboki inda yace zasu sake haduwa.
An fice da shugaban Amurka bayan harbin bindiga a jikin katangar fadarsa

An fice da shugaban Amurka bayan harbin bindiga a jikin katangar fadarsa

Tsaro
Jami'an tsaro sun fice da shugaban kasar Amurka daga wajan ganawa da manema labarai bayan harbin bindiga da aka yi a kofar fadarshi.   Bayan wasu mintuna da yin harbin, shugaban kasar ya koma wajan ganawa da manema labaran inda ya bayyana cewa, wanine aka gani da makami kuma an harbeshi a wajen fadar. Yace an yi harbe-harbene kuma an tafi da wani Asibiti amma dai bai san a wane hali wanda aka tafi dashi Asibitin yake ba.   Saidai daga baya hukumar 'yansandan farin kaya ta kasar ta bayyana cewa mutane 2 ne suka jikkata a harbin da aka yi daf da fadar saidai ba'a samu shiga cikin fadar ba.
Mutane 289 da Suka Makale A Kasar Amurka Ake Zaton Zasu Iso Gida Najeriya A Yau

Mutane 289 da Suka Makale A Kasar Amurka Ake Zaton Zasu Iso Gida Najeriya A Yau

Siyasa
Akalla ‘yan Najeriya 289 da suka makale a kasar Amurka sakamakon rufewar kan iyaka da ke fama da cutar corona sun dawo gida. Wani jirgin saman fasinja na Habasha wanda ke dauke da wadanda aka kwashe daga jirgin ya tashi daga New Jersey a ranar Talata da daddare ana sa ran sauka a Filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja da yammacin Laraba. Wannan shine kari na hudu wajan kwashe mutanin, wanda ke kawowa 1,095, adadin yawan 'yan Najeriya da suka makale wadanda Gwamnatin Tarayya ta maido da su daga Amurka. Mutane biyu da suka fito daga gida daya, an sauke su daga wannan jirgin, in ji Ofishin Jakadancin Najeriya a New York, inji Benaoyagha Okoyen. Okoyen ya ce an hana su shiga jirgi saboda gaza gabatar da sakamakon gwajin cutar corona, wanda shine babban abin da ake bukata...
Shugaba Buhari yawa kasar Amurka ta’aziyyar mutuwar wasu ‘yan kasarta 2

Shugaba Buhari yawa kasar Amurka ta’aziyyar mutuwar wasu ‘yan kasarta 2

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya aikewa kasar Amurka da ta'aziyyar wasu 'yan kasar masu fafutuka 2 da suka mutu, John Roberts Lewis, da Rev. Cordy Tindell.   Shugaban a sakon da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya bayyana marigayan 2 a matsayin wanda ke son ci gaba. Ya kuma bayyana cewa Lewis da Dintell sun yi aiki sosai wajan ganin bakar fata sun samu 'yanci a kasar Amurka da sauran kasashen Duniya.
Hotuna: ‘Yan Najeriya da suka makale a Amurka, Gwamnati ta tura jirgi a kwasosu, sun iso Abuja

Hotuna: ‘Yan Najeriya da suka makale a Amurka, Gwamnati ta tura jirgi a kwasosu, sun iso Abuja

Siyasa
Wasu daga cikin 'yan Najeriya da suka makale a kasar Amurka, gwamnati ta tura jirgin sama ya daukosu sun dira a Abuja, babban birnin Najeriya.   Matafiyan sun sauka ne a jiya, Asabar, kamar yanda Hukumar kula da 'yan Najeriya dake kasar waje ta bayyana.   Hakanan duka an musu gwaji kuma basa dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 amma duk da haka an killacesu na tsawon kwanaki 14, kamar yanda doka ta tanada.