
Jami’an ‘yansanda sunyi nasarar cafke wani Barawo bayan da yayi fashin wayar hannu mallakar wata
Wani matashi mai shekaru 23 mai suna Ikechukwu Jude dan asalin jihar Enugu ya shiga komar Jami'an 'yan sanda, bayan da akai zarginshi da yin fashin wayar hannu mallakar wata mata wacce darajar wayar ta kai kimanin N45.
Lamarin dai ya farune ne a kauyan Amakwu dake karamar hukumar Ekwusigo a jihar Anambra, inda Matshin yayi sa'ar yiwa matar kwacen waya.
Tun dai da fari matar mai suna Jennifer Okwueze ta kai rahoton kwacanne zuwa ga ofishin hukuma inda ta sanar da cewa, an yi mata fashin waya.
A cewar, mai magana da yawun hukumar 'yansanda Haruna Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa tuni sunyi nasarar cafke dan fashin, haka zalika hukuma zata gudanar da bincike tare da gurfanar da mai laifin don girbar laifin daya aikata.