fbpx
Monday, May 23
Shadow

Tag: Anambara

Mutane 13 sun tsallake rijiya da baya a wani hadarin mota da ya faru a jihar Anambara

Mutane 13 sun tsallake rijiya da baya a wani hadarin mota da ya faru a jihar Anambara

Uncategorized
A kalla Mutane 13 ne a ranar Litinin da yammaci suka tsallake rijiya da baya a wani hadari da ya faru a jihar Anambra. Da take tabbatar da faruwar lamarin a  wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Florence Edor, ta ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 1:40 na dare a yankin Upper Iweka da ke cikin garin. Hatsarin ya rutsa da wani direban motar Toyota Harrier Jeep mai lamba AAA 935 FN, da wani direban da ba a bayyana  ko wanene ba a wata motar bas. A cewar Jami'in  jimillan mutane goma sha bakwai ne suka yi hatsarin wanda ya kunshi maza manya da mata manya bakwai da yaro daya. Hakanan suma Wasu shaidun gani da Ido sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka bayyana cewa lamarin ya faru ne a sakamakon gudun wuce sa'a. Sai dai ba'a...
Hukumar Zabe ta sanya ranar 6 ga Nuwamba a matsayin ranar zaben gwamna a jihar Anambra

Hukumar Zabe ta sanya ranar 6 ga Nuwamba a matsayin ranar zaben gwamna a jihar Anambra

Siyasa
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta sanya ranar 6 ga Nuwamba, 2021, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra. Sanarwar na kunshe ne ta cikin jawabin da Shugaban masu wayar da kan masu zabe Festus Okoye ya fitar. Hukumar zaben ta bukaci jam'iyyun siyasa dasu gudanar da zabukan fidda gwani akan ka'ida batare da son rai ba. Hakanan hukumar ta fitar da Jaddawalin zabukan fidda gwani inda ta sanya ranar 6 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a gudanar da babban zaben gwamnan jihar.
‘Yan sanda sun ceto wani Jariri Sabuwar haihuwa Da aka yasar Dashi A Jihar Anambra

‘Yan sanda sun ceto wani Jariri Sabuwar haihuwa Da aka yasar Dashi A Jihar Anambra

Uncategorized
Jam'an 'yan sanda sun ceto wani jariri sabuwar haihuwa da aka ya sar dashi a nannade a cikin zani a wani kwalbati da ke yankin Abuja Estate a Awka, babban birnin jihar Anambra, in ji kakakin‘ yan sanda Haruna Mohammed a  wata sanarwa da ya fitar a jiya. Mohammed ya bayyana cewa, duk  kokarin da aka yi don gano mahaifiyar jaririn amma hakan ya ci tura. A cewar sa, bayan rahoton da Jami'an 'yan sanda su ka samu, sun ziyarci wurin inda su kai nasarar ceto jaririn, wanda ke cikin koshin lafiya," in ji shi. A ranar 3 ga Oktoba ne Wani mazauni a yankin Awka ya bada rahoto a  ofishin 'yan sanda dake a yankin game da jaririn da aka yasar. Muhammad kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya tabbatar da cewa, tuni rundunar ta kai jaririn zuwa Asbitin kula da yara wanda daga bisani rundunar za...