fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Anambra

Wasu ‘yan bindiga a jihar Anambra sun harbe mutane Uku

Wasu ‘yan bindiga a jihar Anambra sun harbe mutane Uku

Crime
Rahotanni daga jihar Anambra na nuni da cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun harbe mutum uku. 'Yan bindigar an shaida cewa sun zo ne a cikin wata Mota kirar Mercedes V. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, CSP Haruna Mohammed, ya ce rundunar ta sha alwashin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika. Dan haka rundunar ta bayyana sunayen wadanda abin ya rutsa dasu kamar haka, “Izuchukwu Idemili mai shekaru 32 da, Chidi Oforma 'mai shekaru 31 da Bongo Muoghalu' mai shekaru 45.  
Hotuna: Wani yaro ya gamu da Ajalinsa bayan da wani Direban mota ya bugi shi

Hotuna: Wani yaro ya gamu da Ajalinsa bayan da wani Direban mota ya bugi shi

Crime
Al'amarin dai ya faru ne a jihar Anambra inda wani Direban Mota wanda aka gaza bayyana sunan sa yayi Awon gaba da wani karamin yaro a sanadin tsananin gudu da Dirban motor ke yi akan titi. Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2 na ranar Talata a dai-dai lokacin da yaron yayi kokarin tsallaka titi inda Dirban motar yayi ciki dashi kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida faruwar lamarin. Bayan kokarin ceto yaron amma ina lokacin da aka isa dashi zuwa Asbiti tuni rai yayi halinnasa kamar yadda hukumar Kiyaye hadura ta tabbatar da al'amarin. Suma wasu Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, hatsarin ya faru ne a sakamakon gudun wuce sa'a da Direban da ake zargi yake yi akan titi.
Wata Mata ta yi yunkurin saida Jaririnta dan watanni Uku da haihuwa kan kudi Naira N150,000 saboda kuncin rayuwa

Wata Mata ta yi yunkurin saida Jaririnta dan watanni Uku da haihuwa kan kudi Naira N150,000 saboda kuncin rayuwa

Crime
Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra, ta cafke wata mata‘ yar shekara 21, Emila Sunday, tare da wani jariri dan wata uku bisa yunkurin sayar da jaririnta kan kudi Naira N150,000. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Haruna Mohammed, shine ya tabbatar da hakan a  wata sanarwa da ya fitar, inda ya shaida cewa,  Rundunar tai nasarar cafke matar ne a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar, 2020, da misalin karfe 6:00 na yamma, bayan rahotannin sirri da jami'an' yan sanda da ke Ojoto Division a jihar suka samu. Mohammed ya ce binciken farko da rundunar ta gudanar ya gano cewa matar na kokarin sayar da dan nata ne sakamakon taulaci kamar yadda Matar ta bayyana. A halin yanzu, an ceto jaririn cikin koshin lafiya kuma ana ci gaba da bincike don gano yadda lamarin ya faru.
Wata mata ta rasa ranta bayan da wani Direban mota yiyi Awon gaba da ita A jihar Anambra

Wata mata ta rasa ranta bayan da wani Direban mota yiyi Awon gaba da ita A jihar Anambra

Crime
Wata mata mai matsakaicin shekaru, ta gamu da A jalinta a dai-dai lokacin da wani Direban Mota da ke matsanan cin gudu a kan hanya  ya murkushe ta wanda hakan yayi sanadin mutuwarta. Lamarin dai ya faru ne, a ranar Talata a Onitsha dake jihar Anambra, kamar yadda wadanda abin ya faru a kan idanunsu, suka bayyana cewa, Direban ya buge matar ne a lokacin da ya ke tuki matsanan ci, kafin daga bisani Jami'an hukumar kiyaye hadura su kai ga ceto matar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin wani Jami'in hukumar kiyaye Hadura Ag Kamal Musa ya sahida cewa hukumar ta yi nasarar kai matar zuwa Asbiti dake Onitsha wanda daga bisani likitoci su ka tabbatar da mutuwar ta. Shima da ya ke martani Kwamandan reshen jihar, FRSC, Mista Andrew Kumapayi, yayin aika sakon ta'aziya ga dangin mamacin, ya g...
Dan takarar Gwamnan Anambra yace idan aka zabeshi zai gina Jami’o’i 21, hakan yasa ana ta mai ba’a

Dan takarar Gwamnan Anambra yace idan aka zabeshi zai gina Jami’o’i 21, hakan yasa ana ta mai ba’a

Uncategorized
Dan takarar gwamnan jihar Anambra wanda Likitane dake zaune a kasar Amurka, ya bayyana cewa idan aka bashi damar zama gwamnan jihar zai gina Jami'o'i 21.   Ya bayyana hakane a wani taron matasa da ya shirya a gidansa inda a karshem makon da ya gabata.   Ya bayyanawa matasan cewa idan suka zabeshi zai tabbatar ya gina Jami'a a kowace karamar hukukq ta jihar, watau guda 21. Yace ba abune me wuyaba. Sunnews ta ruwaitoshi yana cewa a wasu kasashen, gari daya na da Jami'o'i 6. “If given the opportunity, I will build one university each in all the 21 Local Government Areas of the state. Education is key all over the world. We shouldn’t have a few scattered universities here. It is not that hard to set it up.   “In other places of the earth, some towns have...
Mutane shida sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Anambra

Mutane shida sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Anambra

Uncategorized
Mutane shida ne suka mutu, 11 kuma suka jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da wata karamar mota mallakar kamfanin sufuri na CDO mai lamba BGT 313 XA da kuma wata farar mota ba tare da lambar rajista ba a Nteje, kan babbar hanyar Awka - Onitsha. Jami'in Ilimin Jama'a na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa, FRSC, na reshen Anambra, Mista Jamal Musa ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon gudun wuce gona da iri da ya kai ga rasa kulawar motar bas din.   Six persons were killed and 11 injured in an auto crash involving a minibus belonging to CDO Transport Company with registration number BGT 313  XA and a white truck without a registration number at Nteje, along Awka – Onitsha expressway.   Public Education Officer of the Federal Road Safety Commission, FRSC, for Anam...
Fasinjoji sun kone kurmus bayan hatsarin Anambra>>FRSC

Fasinjoji sun kone kurmus bayan hatsarin Anambra>>FRSC

Uncategorized
Mista Andrew Kumapayi, kwamandan reshen jihar Anambra na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa, ya fada a ranar Lahadi cewa fasinjoji da yawa sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba lokacin da motarsu ta kama da wuta a kan hanyar Ihiala zuwa Onitsha a jihar ta Anambra. Kumapayi ya ce har yanzu ba su san ainihin adadin mutanen da suka mutu a hatsarin ba saboda sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba. “A yammacin yau, wani hatsarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane wanda ake zargin fashewar tayoyi ne sakamakon tsananin guda, kuma suka kama da wuta. “Bayanai da ke zuwa ga rundunar sun bayyana cewa dukkan fasinjojin da ke ciki sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba, tare da motar bas din. Kumapayi ya ce, an ijiye gawarwakin wadanda suka mutu dakin ajiyar gawarwaki ...
An kama wata Inyamura da kananan Yaran da aka sato daga Jihar Gombe

An kama wata Inyamura da kananan Yaran da aka sato daga Jihar Gombe

Uncategorized
Hukumar 'yansandan jihar Anambra ta tabbatar da kama wata mata, Nkechi Odinye me shekaru 55 dake dillancin safarar kananan yara.   Kakakin 'Yansandan jihar, Haruna Muhammad ya bayyana cewa, wasu ne da aka kama suka tonawa matar Asiri. Hutudole ya fahimci yaran da aka  gano wata matace me suna Hauwa Musa ta satosu daga Gombe ta kaiwa matar a jihar Anambra. Rahoton ya bayyana cewa Inyamurar na sayen yaran akan Dubu Dari 2 zuwa Dubu dari 4, ya danganta da shekaru da kuma jinsin yaran da aka sato.   Ya kara da cewa sun kama Inyamurar ne a Obosi dake karamar hukumar Idelimi North a Jihar ta Anambra, bayan samun bayana sirri an kuma gano yara 12 tare da ita 8 maza 4 mata. Yace ta shafe shekaru 3 tana zillewa 'yansandan sai ranar 31 ga watan Augusta Allah yayi ala kam...
Minista Ngige ya goyi bayan dakatar da sarakunan Anambra saboda sun je gaida Shugaba Buhari

Minista Ngige ya goyi bayan dakatar da sarakunan Anambra saboda sun je gaida Shugaba Buhari

Siyasa
Ministan Kwadago, Chris Ngige ya bayyana cewa yana goyon bayan dakatarwar da gwamnan jihar Anambra,  Willie Obiano yawa sarakunan gargajiya 12 da suka je gaishe da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Abuja.   Gwamnan ya dakatar da sarakunanne saboda kamin su tafi Abuja basu nemi izininsa ba kamar yanda yake a doka. Hutudole ya samo muku cewa a hirar da yayi da Punch, Chris Ngige ya bayyana cewa dakatarwar da akawa sarakunan ta yi kadan. Yace ya kamata a kori sarakunan daga garuruwansu saboda gudun tada fitina. Ya kuma bada shawarar cewa ya kamata shima dan kasuwar da ya musu jagora zuwa wajan shugaban kasar, Prince Arthur Eze shima a hukuntashi.
Gwamnan Anambra ya dakatar da sarakuna 12 saboda kaiwa shugaba Buhari ziyara

Gwamnan Anambra ya dakatar da sarakuna 12 saboda kaiwa shugaba Buhari ziyara

Siyasa
Gwamnan jihar Anambra,  Willie Obiano ya dakatar da wasu sarakuna 12 a jiharsa saboda kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara.   Dakatarwar na zuwane saboda Sarakunan sun fita daga jihar ba tare da sanar da gwamnati ba, kamar yanda sanarwar ta bayyanar. Hutudole ya fahimci dakatarwar zata yi aiki ne nan da shekara 1. Sannan ana so duka sarakunan da aka dakatar din su daina duk wani aiki irin na sarki a ciki da wajen jihar sannan kuma nan da shekara 1 idan sun bi wannan doka to za'a iya dage dakatarwar ko kuma ta ci gaba da aiki idan aka samesu da taka wannan doka.