
Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da sakawa Najeriya matsin lamba a yafewa wanda yayi batanci ga Addini a Kano
Wasu ƙwararru kan kare haƙƙin bil adama a Majalisar Dinkin Duniya sun buƙaci a saki ɗan Najeriyar nan da aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda yin ɓatanci ga addini.
An yanke wa matashin Yahaya Sharif-Aminu mai shekara 22 hukuncin ne ranar 10 ga watan Agusta bayan samunsa da yin ɓatanci cikin wata waƙa da ya yi.
Cikin wata sanarwa, ƙwararrun su 10 sun nemi a soke hukuncin inda suka ce tun farkon shari'ar matashin bai samu lauyan da zai kare shi ba.
A cewarsu, yin waƙa ba laifi bane.
Shi ma Daraktan kula da gidan tarihin Auschwitz, tsohon sansanin ƴan Nazi a Poland ya buƙaci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yafe wa yaron da ya yi ɓatanci ga addini a Kano.
Dakta Piotr Cywinski, ya ce shi da wasu ƴan sa-kai 119 daga sassan duniya za su yi wa yaron zaman gidan yari na w...